Majalisa ta gargadi 'yan Nigeria kan amfani da kudin intanet, Bitcoin

bitcoin

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar dattawan Najeriyar ta nuna matukar damuwarta a kan yadda ake jan hankalin 'yan kasar don rungumar tsarin amfani da kudin intanet na Bitcoin din, musamman a matsayin wata hanyar zuba jari da ke rubbanya riba cikin sauri.

Majalisar ta nuna damuwar ne bayan wata muhawara a ranar Talata a kan wani kudurin da wani dan majalisar, Sanata Benjamin Uwajumogu ya gabatar.

Majalisar ta ce tana sane da cewa jaridar The guardian ta Amurka ta taba wallafa cewa, babban bankin zuba jarin nan na duniya, JP Morgan, ya bayyana cewa kudin gizon ya fi dacewa da masu safarar miyagun kwayoyi kuma ba zai kai labari ba.

Haka kuma babban bankin Najeriya wato CBN bai amince da amfani da kudin na Bitcoin a hukumance ba, duk kuwa da cewa bankin da kasuwar shunku ta kasa da kuma hukumar inshora ta kasa ba su yi wani hobbasa ba na wayar da kan jama'a a kan hadduran da ke tattare da kudin gizon.

Majalisar dattawan ta kuma yi la'akari da cewa a shekarar 2016 miliyoyin 'yan kasar sun yi asara, inda har ta kai wasu ma suka rasa jarinsu dungurungum a sanadin tsarin nan na MMM.

Sannan ganin kasar na farfadowa ne daga matsin tattalin arzikin da ta shiga, majalisar ta nuna damuwar cewa tsarin amfani da kudin gizon zai iya mummunan tasiri idan mutane suka yi asarar kudaden shigarsu.

Hasalima dai tsarin zai iya illa ga tattalin arzikin kasar saboda za ta iya asarar kudaden asusun ajiyarta na kasashen waje.

bitcoin

Asalin hoton, Getty Images

A don haka, wadannan dalilai da ma wasu ne suka sanya majalisar ta bukaci CBN da hukumar inshora ta kasa NDIC, da hukumar wayar da kan al'umma, su yi gagarumar yekuwa ga 'yan kasar don fadakar da su hadarin da ke tattare da amfani da kudin na Bitcoin.

Haka kuma majalisar ta bai wa kwamitinta kan fannin banki da sauran hukumomin hada-hadar kudade makonni biyu ya yi bincike a kan ko za a iya amfani da Bitcoin wajen zuba jari da hanyoyin da za a iya sa ido a kan masu cinikayya da shi.

Sai dai masu iya magana na cewa abincin wani gubar wani, a yayin da wasu ke dari-dari dn amfani da kudin gizon, wata kungiyar kwallon kafa a Turkiyya ta bugi kirjin zama kungiya ta farko da ta sayi Omer Faruk Kıroglu da kudin na intanet wanda darajarsa ta kai sama da fam 384.

Kuma a baya-bayan nan ne kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shiga wata yarjejeniya ta daukar nauyin da kuma sanya sunan kamfanin kudin intanet na Cashbet a jikin rigar 'yan wasa.