An raba 'yan biyun da aka haifa a hade

Likitoci sun ce an yi nasarar yi wa 'yan biyun nan da aka haifa a hade na Gaza tiyata kuma an gama lafiya.

Jariran duka mata ne masu suna Farah da Haneen, an yi musu tiyatar ne a asibitin yara na King Abdullahi da ke birnin Riyadh.

Kafafun jariran a hade suke amma zuciyarsu da huhunsu a rabe.

An dawo da jariran Saudiya ne tare da mahaifinsu, bayan da likitoci suka yi gargadin cewa rayuwarsu za ta iya shiga hadari idan suka ci gaba da zama a Gaza.

An haifi yaran ne a watan Oktoba, kuma cikinsu da jikinsu a hade yake.

A wani bayani da kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya fitar likitocin sun bayar da sanarwar cewa anyi tiyatar cikin nasara.

Inda suka ce tiyatar na bukatar a raba musu hanji, da hanta da kuma kugunsu.

A watan Disamba ne aka kai jariran Saudiyya domin yi musu tiyatar, bayan da aka dauko su daga Gaza zuwa Jordan, in ji kafar watsa labaran Saudiyyar inda Majalisar dinkin duniya ta ce an samu koma a fannin harkokin lafiya sakamakon takunkumin da aka sa musu, da sauran tashe-tashen hankula.

Isra'ila da Masar sun fuskanci takunkumi daga Gaza tun tsawon shekaru da dama, a kokarin da suke na hana kai hare-hare daga mayakan da suke yankin.