Mece ce makomar Robert Mugabe bayan kwace masa iko?

    • Marubuci, Daga Lebo Diseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Bayan da ya shafe shekara 37 kan mulki a Zimbabwe, a yanzu an yi wa Robert Mugabe daurin talala bayan da sojoji suka kwace iko a kasar.

Jami'an diflomasiya daga kasashen kudancin Afrika da wani shugaban babbar cocin a Zimbabwe na kokarin shiga tsakani domin yin sulhu tsakaninsa da sojojin kasar.

Shin ko mece ce makomar Shugaba Mugabe da kuma Zimbabwe?

Ga dai wasu abubuwa da ake ganin za su iya faruwa.

1:Mugabe ya yi murabus

Bayan wasu sa'oi da Manjo Janar Sibusiso Moyo ya yi shelar cewa sojoji sun kwace iko a gidan talibiji na gwamnati, an dinga jita-jitar cewa Shugaba Mugabe mai shekara 93 shi ma zai yi wa al'ummar kasar jawabi, inda zai sanar da cewa ya yi murabus.

Wannan dai bai gamsar ba, amma ana ganin abu ne da zai iya faruwa.

Haka kuma wannan zai bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa damar darewa kan kujerar shugaban jam'iyyar Zanu-PF mai mulki.

An yi amannar cewa korarsa da aka yi a makon da ya gabata, ita ce dalilin da ya sa sojojin kasar suka dauki wannan mataki.

2: Mugabe ya ci gaba da zama kan mulki

Kawo yanzu sojoji na ci gaba da kiran Robert Mugabe, "Mai shugaban kasa".

Da dama daga cikin sojojin kasar da kuma 'ya'yan jam'iyyar Zanu-PF me mulki na goyon bayan shugaba Mugabe.

Ba su da matsala da shi, sai dai ba su gamsu da abin da suka dinga gani ba, watau yunkurin karbe iko na matarsa, Grace, wadda take son ta gaje shi.

Wakilin Zanu- PF a Birtaniya, Nick Mangwana, ya shaidawa BBC cewa Mr Mugabe zai ci gaba da rike mulki har sai bayan an kammala babban taron jam'iyyar da za a yi a watan Disamba mai zuwa, a lokacin da watakila za a rantsar da Mr Mnangagwa a matsayin shugaban jam'iyyar da kuma na kasa.

Sai dai kamfanin dillanci labaru na Reuters ya ruwaito cewa shugaba Mugabe ya nanata cewa zai kammala sauran wa'adinsa kan mulki.

Wannan zai ba shi damar tsayawa har sai bayan zaben shugaban kasa da za a yi a badi.

3. An tilastawa Mugabe gudun hijira

Shin ko mene ne zai faru idan 'ya'yan jam'iyyar Zanu PF suka kasa cimma matsaya? Toh watakila hakan zai sa Shugaba Mugabe ya yi gudun hjira.

Makwabciyyar kasar, Afrika ta Kudu za ta iya kasancewa wurin da zai iya samun mafaka, sai dai lamura sun sauya a baya-bayan nan.

Ana girmama Mr Mugabe a Afrika ta Kudun, saboda rawar da ya taka wajen kawar da mulkin wariyar launin fata.

Tuni jam'iyyar adawa ta EFF ta nemi gwamnatin kasar a kan ta shirya wajen yi masa "maraba idan ya nemi mafaka."

Rahotani sun ce iyalin Mugabe sun mallaki kadarori a Afirka ta Kudu.

Sai dai tambayar a nan ita ce, shin ko ya ya makomar Grace matarsa za ta kasance?

An dai ba ta damar amfani da rigar kariya ta diflomasiya game da zargin cin zarafin wata mata mai tallata kayan kawa a wani otal a watan Augustan da ya gabata a birnin Johannesburg.

Sai dai Gabriella Engels na kokarin ganin cewa ta jingine rigar kariyar, kuma wannan na nufin cewa Grace Mugabe za ta iya fuskantar sharia idan ta nemi mafaka a Afrika ta Kudu.

Shin ina za ta je ban da Afrika ta Kudu?

Watakila ta je Singapore ko Malaysia, wadanda kasashe ne da iyalin Mugabe suke da kadarori.

4. Gwamnatin hadin giwa da kuma zaben shugaban kasa

Jogoran 'yan adawa na jam'iyyar MDC- Morgan Tsvangirai, ya koma Harare bayan ya dawo daga jinyar da ka yi masa kan cutar sankara a kasar Afrika ta Kudu, abin da ya kara ruruta rade-radin da ake yi a kan cewa wata kila za a yi tattaunawar kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Ana dai ganin kasashen yamma da dama da kuma 'yan adawa za su amince da wannan mataki.

Wani jagoran 'yan adawa, Tendai Biti, ya ce zai shiga cikin jam'iyyar hadin gwiwar idan Mr Tsvangirai na ciki.

5: Shin Mugabe ya sauya hali ne?

Sai dai ikon da sojoji suka kwace, ba wai yana nufiin an samu sabuwar gwamnati ba ce. Takaddama ce ta cikin gida tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Zanu-PF kuma har yanzu ita ce take rike da mulki a kasar.

Haka kuma ana ganin rundunar sojin kasa kamar wani reshe ne na jam'iyyar ta Zanu-PF.

Kuma mutumin da suke marawa baya, Emmerson Mnangawa ya taimaka wa Robert Mugabe wajen aiwatar da wasu sauye-sauye da suka rika janyo ce-ce-ku-ce.

Wasu sun ce ya fi Shugaba Mugabe iya rashin mutunci.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayyani kan ko idan an kifar da gwamnatin Mugabe, hakan zai inganta rayuwar 'yan kasar.

6: Mugabe ya mayar da martani kan juyin mulki da aka yi masa

Jami'an tsaron da ke gadin fadar shugaban kasa na cikin sojojin da ke yi wa Mugabe biyayya.

An yi wa wurin da suke zama kawanya lokacin da sojoji suka kwace iko.

Sai dai a wani mataki da ba kasafai ake gani ba, masu rike da mukaman janarar-janarar ne suka jagoranci karbe iko a Zimbabwe.

Wasu manyan kusoshi 90 a rundunar sojin kasar suka tsaya tare da Janar Contantino Chiwenga a makon da ya gabata, lokacin da ya yi gargadi a kan abubuwan da ka iya biyo baya game da korar da aka yi wa Mr Mnangagwa.