Nigeria: Gobara ta cinye shaguna a kasuwar Nguru

Wata mummunar gobara ta cinye shaguna da dama a babbar kasuwar garin Nguru da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda wani ganau, Sani Ballack, ya shaida wa BBC ta waya.

Ya ce "gobarar wadda ta cinye shaguna akalla 500 ta jawo mummunar asara ga 'yan kasuwa, kodayake ba a samu asarar r ai ba, sai dai jikkata"

Har ila yau ya ce gobarar wadda ba a samu an kashe ta ba har zuwa safiyar Asabar ta samu asali ne "daga tattatsin wayar wutar lantarki."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Yobe DSP, Jafiya Zubairu, ya tabbatar da faruwar al'amarin.

Sai dai ya ce bai san girman barnar da aka tafka ba a kasuwar.

Ana sayar da atamfofi ne da turare da kayan gine-gine da dai sauransu a kasuwar.