Ruwan sama ya hallaka mutum shida a wasu kasashen Turai

Asalin hoton, Reuters
Ruwa da iska mai karfin gaske sun yi kaca-kaca da wasu bangarori na yankin tsakiya da na arewacin Turai, inda har ya jawo mutuwar a kalla mutum shida a Jamus da Poland da kuma Jamhuriyar Czech.
Cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da wani dan shekara 63 da ya yi sansani ya yada zango a bakin gabar teku a Jamus, da kuma wasu 'yan yawon bude ido biyu.
Karfin gudun iskar ya kai kilomita 180 a sa'a daya inda har ta kai nisan tsauni mafi tsawo a kasar Czech.
Daruruwan 'yan kasar Poland da Czech sun kasance har yanzu babu wutar lantarki, yayin da aka samu ambaliyar ruwa a yankin tsakiyar birnin Hamburg na Jamus.
An dakatar da sufuri ta hanyoyin jirgin kasa a wasu yankunan na Jamus saboda lalacewar hanyoyi.
An sanar da yankewar layukan dogo da kuma hanyoyi a cikin kasar Czech.
Faduwar bishiyoyi saboda karfin iskar a Jamus da Czech da kuma Poland ya yi sanadiyyar mutuwar jama'a da dama.
A Jamus, rahotanni sun ce wata mata 'yar shekara 48 da kuma wani namiji mai shekara 56 sun mutu bayan da jirgin ruwa ya tuntsure da su a jihar Mecklenburg-Vorpommern, da ke arewacin kasar.
Amma har a ranar Litinin ana ci gaba da neman mutum na uku da ya bace.
Ambaliyar ta zagaye wata kasuwar sayar da kifi a Hamburg.
Da akwai fargaba game da yanayin da wajen ajiyar man fetur na Jamus ya ke ciki a Glory Amsterdam da ke arewacin tekun kasar.
Hukumomi na sa ido don gane alamun yoyo da ma'ajiyar man ka iya yi, mai yawan tan 1,800.
Ana kokarin kai dauki ga wani gungun masu aikin jirage su 22 da ba su ji rauni ba domin ceto su, to sai dai karfin igiyar ruwan na kawo cikas ga kokarin da ake yi.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, AFP











