Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya
Wasu zababbun hotuna daga nahiyar Afirka da kuma na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya.

Asalin hoton, AFP
An haska filin wasanni na Mohamed VI a birnin Casablanca da wuta mai launin ja a ranar Asabar a yayin da magoya bayan kungiyar kwallon kafar Morocco mai suna Wydad Casablanca suka doke kungiyar kwallon kafar Algeria mai suna USM Algerm inda suka kai matakin karshe a wasan zakarun Afirka.

Asalin hoton, AFP
Kayan wata 'yar Najeriya Amede, mai dinka kayan kawa sun kayatar ranar Laraba a bikin baje kolin kayan kawan a jihar Legas, wanda zai taimaka wajen tallafawa da kuma inganta masana'antun kayan kawa a Najeriya da ma Afirka.

Asalin hoton, Reuters
Zaman lafiya a Kenya, shi ne jigo ga wadannan maza da suke daukar hoto a lokacin bikin ranar jarumai ta kasar a babban birnin Nairobi ranar Juma'ar da ta gabata wacce ta kasance ranar hutu ce.

Asalin hoton, AFP
Sai dai kuma banga da tashin hankali sun gabaci maimaicin zaben shugaban kasar- a wannan hoton, wani mutum ne rike da sandar da take ci da wuta inda magoya bayan 'yan adawa suka yi zanga-zanga a wajen shingaye masu ci da wuta a wani yankin marasa galihu na Kibera a birnin Nairobi ranar Laraba.

Asalin hoton, Reuters
Ranar Alhamis, wadda ta kasance ranar zaben, tashin hankalin ya ci gaba: A wannan hoton, wani mutum ne yake hangen arangamar da ake yi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a garin Kibera.

Asalin hoton, AFP
A yayin da su kuma wadannan mabiya cocin Kenya na Legio Maria suka shiga matsi lokacin da aka harba hayaki mai sa hawaye lokacin arangama a unguwar Mathare a Nairobi ranar zabe.

Asalin hoton, Reuters
'Yan ci rani sun zauna a jere ranar Asabar yayin da suke jiran samun aiki a birnin Misrata na Libya.

Asalin hoton, Reuters
Wata yarinya 'yar gudun hijira daga Sudan ta Kudu a sansanin 'yan gudun hijira a Nguenyyiel ranar Talata, a lokacin da Jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya ya kai ziyara yankin Gambella a Kasar Ethiopia.

Asalin hoton, EPA
Wani taron tunawa da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela mai taken 'Mandela Walk Together' a Westminster birnin London ranar Litinin wanda ya samu halartar matar marigayin, Grace Machel, da tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan da ma wasu sanannun mutane a duniya.

Asalin hoton, Reuters
Wani dan kasar Birtaniya Tom Morgan ya gwada wani abu da ba a taba ganin irinsa ba inda ya tashi sama tsawon kilomita 25 da taimakon balan-balan guda 100 da ya daura a jikin kujerar da yake zaune a kai.

Asalin hoton, EPA
Wani dan kasar Afirka ta Kudu Mike Schlebach ya taka rawa a gasar zamiyar cikin ruwa a birnin Cape Town ranar Litinin.
Hotuna daga AFP da EPA da PA da kuma Reuters











