Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zakaran kwallon kafar Afirka na 2017
Za a sanar da sunayen 'yan wasan da aka tace don bai wa daya daga cikinsu kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2017 a wani shiri na musamman da za a gabatar kai-tsaye sashen BBC World Service mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya, da tashar talabijin ta BBC World News da shafukan BBC na intanet da kafofin sada zumunta.
Za a soma yada shirin ne daga karfe 6:05 na yamma agogon GMT, zuwa karfe 7:00 na yamma agogon GMT, a ranar 11 ga watan Nuwamban 2017.
Za a bude shafin kada kuri'a da misalin karfe 6:50 na yamma agogon GMT.
Ga kuma ka'idojin zaben a kasa.
Tsarin da aka bi wajen zabo jerin sunanyen 'yan takarar:
Kwararru a harkar kwallon kafa a ciki da wajen Afirka ne suka zabo 'yan takarar biyar, bayan da aka bukace su da su lissafa fitattun 'yan wasa biyar, kuma su jera su daga 1 zuwa 5, (wanda ya fi burge su shi ke da maki biyar).
An kuma bukace su da su yi amfani da ma'aunan da ke kasa wajen zabo gwanayen nasu:
*** Bajinta wajen taka leda (wato iya sarrafa kwallo da kwazo da hadin kai da sauran 'yan wasa, da taka rawa wajen samar da sakamako mai kyau, da lambobin yabo, da hazaka a daukacin shekarar 2017, da kuma inganta wasa).
*** Tasiri a yankin da dan wasa ya fito (wato gudunmuwar da dan wasan ya bayar ga fannin kwallon kafa da ma wasanni baki daya a yankin da ya fito, a ciki da wajen fili).
*** Muhimmancinsa a duniya (wato muhimmancin da yake da shi a fagen wasan a duniya da kuma cigaban da ya kawo).
An kuma bukaci kwararrun da su yi la'akari da shekarar bana, (daga ranar 1 ga watan Junairun 2017, zuwa yanzu).
Za sanar da jerin sunayen 'yan wasan ne yayin wani shiri na musamman na kaddamar da gasar a ranar 11 ga watan Nuwamba, daga karfe 6:00 na yamma, zuwa karfe 7:00 na yamma agogon GMT, a tashar rediyo ta BBC World Service da tashar talabijin ta BBC World TV.
Za kuma a wallafa shirin a shafin mu na BBC Hausa.com da kuma sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC. http://www.bbc.co.uk/sport/football/african
Idan kuma 'yan wasa biyu suka yi kankankan, to jami'an da ke shirya Gasar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na da hakkin kara yawan 'yan takarar zuwa adadin da bai haura shida ba.
Ta'arifin wanda ya cancanta:
Duk dan wasan da ya cancanci shiga tawagar wata kasar Afirka, ya cancanci ya lashe kyautar Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC.
Kada kuri'a:
Da zarar an wallafa sunayen 'yan wasan da suka cancanta, ma'abota shafukan BBC za su kada kuri'a don zaben wanda za a baiwa gasar.
Za a soma zabe da misalin karfe 6:50 na yamma agogon GMT a ranar 11 ga watan Nuwamban 2017, kuma a rufe ranar 27 ga watan Nuwamba 2017 da misalin karfe 6:00 daidai na yamma agogon GMT.
A ranar 11 ga watan Disamba na 2017 ne da misalin karfe 5:35 na yamma agogon GMT kuma za a sanar da sakamakon zaben kai-tsaye a tashar talabiji da ta rediyo ta BBC Focus on Africa da shafin intanet na BBC Hausa, wato bbchausa.com.
Za kuma a wallafa a sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC http://www.bbc.co.uk/sport/football/african tare da ka'idoji da sharuddan gasar.
Idan aka samu 'yan wasan da suka yi kankankan, za su raba kyautar.
Yadda za a kada kuri'a - a intanet
A ziyarci sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC http://www.bbc.co.uk/sport/football/african sannan a bi matakan da aka zayyana.
(Daga shafin mu na BBC Hausa ne za ka latsa:
http://www.bbc.co.uk/sport/football/african wanda zai kai ka shafin wasanni na BBC, inda za ka bi ka'idojin zaben.)
Kuri'a daya kawai za a iya kadawa a kan kowacce komfuta.
Kada Kuri'a: Ka'idoji da sharudda:
1. BBC ce ke kula da kada kuri'a, kuma kyautar ta dace da dokokin BBC game da gasa da kada kuri'a, wadanda za a iya karantawa a nan. http://www.bbc.co.uk/editorialguidelines/guidelines/appendix2
2. Wanda ya lashe gasar zai samu lambar yabo sannan za a yi masa lakabi da "Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2017", wato "The BBC African Footballer of the Year 2017" a Turance.
3. Wani kwamitin masana harkar kwallon kafar Afirka ne ya tsara jerin sunayen 'yan takarar da za a zabi gwarzon daga cikinsu.
4. Ma'aunan da aka yi amfani wajen zakulo wadannan 'yan wasa su ne:
Iya sarrafa kwallo da kwazo da aiki tare da sauran 'yan wasa, da samar da kyakkyawan sakamako, da lambobin yabo, da gudunmuwar da dan wasan ya bayar ga fannin kwallon kafa da ma wasanni baki daya a yankin da ya fito, a ciki da wajen fili, da kuma muhimmancinsa ga wasan a fadin duniya da bunkasa shi a daukacin shekarar 2017.
5. Za a bai wa jama'a damar kada kuri'a a kan jerin sunayen a sashen Kwallon Kafar Afirka na shafin Wasanni na BBC http://www.bbc.co.uk/sport/football/african (da ma shafin BBC Hausa, inda za ku iya shiga shafin wasani na BBC, domin kada kuri'a;
http://www.bbc.co.uk/sport/football/african)
6. BBC za ta yi amfani da bayanan masu kada kuri'a, bisa tanade-tanaden Manufofin Tsare Sirri da na Amfani da 'cookies' http://www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy/privacy-policy da kuma ka'idojin amfani da shafin http://bbc.co.uk/usingthebbc/terms/terms-of-use.
Misali, za mu iya amfani da bayananku wajen tattara kuri'u ko kuma gudanar da bincike a kan duk wata tangarda da ka iya aukuwa wajen yin zabe.
7. Za a rufe kada kuri'a da karfe 6:00 na yamma a gogon GMT a ranar 27 ga watan Nuwamban 2017.
8. Ba za a saurari balle a karbi wani korafi game da sakamakon zaben ba.
9. Wajibi ne a karbi kyautar da aka bayar kamar yadda aka bayyana, ba damar jinkirta ta. Ba za a bayar da kudi a maimakon kyautar ba. Kuma ba za a biya mutum don ya kada kuri'a ba.
10. Daga BBC har masu yi mata kwantiragi, da rassanta da/ko cibiyoyinta, ba wanda zai dauki alhakin ko wanne irin nakasu ko gazawa ko wata matsala game da hawa intanet, ko hanyoyin sadarwa da ka iya haddasa sarayar kuri'a, ko rashin shigarta lissafi.
11. BBC na da ikon dakatar da kuri'a idan ta samu isasshiyar hujjar da za ta kai ga zargin yin magudi ko kuma idan ta yi tunanin an yi yunkurin tafka magudi.
BBC na da ikon musanya hanyar yin zaben a duk lokacin da ta ga akwai bukatar hakan. Don samun damar gudanar da bincike a kan wasu matsaloli da aka iya samu yayin kada kuri'a a bbc.co.uk, BBC ka iya amfani da 'cookies' ko ajiye adireshin intanet na na'ura.
BBC ba za ta wallafa wannan bayani ba, kuma ba za ta bai wa kowa ba kan kowa ba ba tare da izini ba, sai dai kawai idan akwai bukatar yin hakan don tabbatar da aiki da wadannan ka'idoji.
12. Duk wanda ya kada kuri'a a wannan zabe ana dauka ya amince da wadannan ka'idoji da sharuddan kuma ya amince ya yi aiki da su.
A lura, dukkan ma'aikatan BBC da suk wani wanda ke da alaka da shirya wannan Gasa bai cancanci kada kuri'a ba.
13. BBC Afirka ce za ta sa ido kan zaben.
14. BBC na da ikon soke ko wanne dan takara, ko hana shi kyautar a duk lokacin da ta ga dama, idan a ganinta bayar da kyautar ga dan takarar ka iya bata sunan BBC.
15. Tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales na da ta cewa a kan wannan zaben da wadannan ka'idoji.