Kenya: 'Yan sanda sun 'kashe' masu zanga-zanga 30

Wadansu masu zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cikin watan nan ne za a sake gudanar da zaben shugaban kasar bayan soke wanda aka yi a watan Agustan da ya wuce

Akalla mutum 30 ake zargin 'yan sanda suka kashe yayin wata zanga-zanga da 'yan adawa suka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya.

A wani sabon rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar ta ce 'yan sandan kasar ''suna da hannu dumu-dumu''.

Har ila yau, akwai wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba wadanda suke cewa 'yan sandan sun kashe wadansu mutum 17 a birnin.

Suna zargin 'yan sandan da tayar da zaune tsaye ta amfani da karfin da ya wuce kima a yankunan da ake tunani cewa ana tashin hankali.

Kungiyar ta ce 'yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima ne a wuraren da ake zaton rikici.

A makon da ya gabata ne jagoran 'yan adwar kasar, Raila Odinga, ya ce ba zai shiga zaben sugaban kasa da za'a sake yi a cikin wannan watan.

Saboda ba shi da imanin cewa za a yi zabe adalci a zabe, a cewarsa.