Shugaba Buhari ya gana da yara masoyansa

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wadansu yara uku mata kanana wadanda ake cewa masoyan shugaban ne a fadarsa da ke Abuja.
Nicole Benson 'yar shekara 12 wadda ta fito daga jihar Legas da Maya Jamal 'yar shekara uku wadda take zaune a Abuja da kuma Aisha Gebbi mai shekara 10 wadda ta fito daga jihar Bauchi sun isa fadar ne tare da rakiyar iyayensu.

Asalin hoton, Twitter/Bashir Ahmad
Yaran sun kwashe kimanin minti 30 a fadar shugaban kasar.
Kafofin yada labaran kasar sun sha ruwaito labarin daya daga cikin yaran wato Nicole a lokacin zaben shekarar 2015, inda suka ce ta taba tallafa wa shugaban da kudin abincinta.
Ba kasafai dai ake ganin shugaban yana ganawa da kananan yara ba.
Karanta karin wadansu labaran masu kayatarwa

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Asalin hoton, Nigeria Presidency







