Hotunan barnar hari ma fi muni a Mogadishu

Fiye da mutum 300 ne suka jikkata a harin bam din da aka yi a birnin Mogadishu ranar Asabar

Motar kashe gobara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fiye da mutum 300 ne suka jikkata a harin bam din da aka yi a birnin Mogadishu ranar Asabar
Wasu masu bayar da kayan agaji
Bayanan hoto, Wasu mutane sun kai kayan agaji ga wadanda da harin bam din ya rutsa da su, yayin da suke samun kulawa a asibiti
Hoton kwashe baraguzan gini
Bayanan hoto, Wasu ma'aikatan gwamnatin Somalia na kwashe baraguzan gine-gine a inda aka kai harin
Ministan Lafiya kasar Turkiyya Ahmet Demircan lokacin da ya kai ziyara wani asibiti don duba wadansu daga cikin mutanen da harin ya shafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ministan Lafiya kasar Turkiyya Ahmet Demircan lokacin da ya kai ziyara wani asibiti don duba wadansu daga cikin mutanen da harin ya shafa
Kasar Turkiyya ta aika da jirgin soja dauke da magunguna na agaji, kuma za a kwashi mutane 40 da suka jikkata zuwa Turkiyya domin ba su kulawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kasar Turkiyya ta aika da jirgin soja dauke da magunguna na agaji, kuma za a kwashi mutane 40 da suka jikkata zuwa Turkiyya domin ba su kulawa
mata masu zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata sun yi zanga-zanga tare da bayar da gudunmawar jini bayan aukuwar harin a ranar Asabar
Daruruwan mutane ne suka halarci zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daruruwan mutane ne suka halarci zanga-zanga
Wata mota da harin ya lalata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Harin ya auku ne a wani wuri mai cike da hada-hadar jama'a