Mutum 22 sun mutu a turereniya a tashar jirgin kasa ta India

Bayanan bidiyo, Matafiya suna kokarin ceton wadanda suka sami rauni

Wata turereniya a tashar jirgin kasa da ke birnin Mumbai ta janyo mutuwar mutum 22 inda fiye da mutum 30 kuma suka jikkata, in ji jami'ai a kasar Indiya.

Iftila'in ya faru ne a lokacin da ma'aikata ke rububin zuwa wajen aiki da safe a tashar jirgin kasa ta Elphinstone, wacce mahada ce ga manyan layukan jirgin kasa guda biyu na cikin birnin.

Cunkoso ne ya jawo wannan iftila'in saboda yawan mutanen da ke neman fakewa daga mamakon ruwan saman da ya rinka sauka.

An tafi da wadanda suka sami rauni zuwa wani asibiti da ke kusa da tashar kuma manyan jami'an tashar jirgin kasan na wurin domin taimakawa.

Yaya lamarin ya faru?

"Iftila'in ya auku ne a daidai lokacin da ake mamakon ruwan sama na Monsoon a birnin Mumbai, kuma matafiya sun taru a tashar domin neman mafaka.

Sai kawai wadanda ke gaba suka zame, dalilin da yasa na bayansu suka zubo kansu. Daga nan sai aka fara turereniya", in ji Ravindra Bhakar, kakakin kamfanin jirgin Kasa na Indiya a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Mun tabbatar da mutum 22 sun mutu, maza 14 da mata takwas... Kuma wasu fasinjoji 32 sun sami raunuka."

Rescue workers

Asalin hoton, BBC Marathi

Bayanan hoto, Masu aikin ceto sun yi gaggawar zuwa wajen

Akash Koteja na cikin wadanda suka sami rauni, kuma ya ce: "A lokacin jiragen kasa na isa tashar kuma wasu fasinjojin na neman ficewa daga tashar, amma wasu kuma sun hana su ficewa.

"Da wasu suka gwada fita sai aka fara turereniya."

Hotunan talabijin sun nuna wasu matafiya na kokarin ceto abokan tafiyarsu daga cikin wadanda aka danne, kuma wasu ana danna kirjinsu domin a farfado da su.

"Mun saka wadanda suka sami rauni a motoci, da motocin 'yan sanda da motocin daukar ma'aikata wadanda suka tafi da su asibiti cikin gaggawa", in ji daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin kamar yadda AFP ta ruwaito.

Me yasa iftila'in ya faru?

Wani bincike da aka kaddamar ya bankado sanadiyyar wannan hatsarin, amma cunkoso shi ne babban dalilin yawan hadurran da ke addabar hanyoyin jiragen kasan Indiya.

Wakiliyar BBC a Mumbai, Yogita Limaye, ta ce hatsarin ya sake bayyana halin tabarbarewar da bangaren sufuri na birnin Mumbai ke ciki.

Kuma an sha sukar yadda gwamnati ba ta sabunta jirage da taragun da ke safarar miliyoyin fasinjoji a hanyoyin jiragen kasa a kullum.

A relative of a stampede victim grieves at a hospital in Mumbai, India September 29, 2017

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan uwan wadanda iftila'in ya faru sun tafi asibitin domin neman labarin halin da 'yan wansu ke ciki