Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bai dace a ayyana IPOB kungiyar 'yan ta'adda ba — Saraki
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce ayyana kungiyar IPOB mai fafatukar kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda da sojin Najeriya ta yi, bai dace da kundin tsarin mulkin kasar ba.
A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bukola Saraki ya ce dokokin Najeriya sun fitar da matakan da za a dauka kafin a ayyana wata kungiya a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
A makon da ya gabata ne dai rundunar sojin Najeriya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Bukola Saraki ya ce yana fatan cewar Shugaba Muhammadu Buhari, zai fara bin hanyar da ta dace wajen ayyana kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda domin nuna wa duniya cewar Najeriya kasa ce wadda ke bin doka a ko wanne hali.
Saboda haka, Saraki ya ce wadanda suke ta magana a kan wannan su sha kuruminsu.
Kazalika, Sanata Saraki ya ce dole a jinjina wa rundunar sojin Najeriya kan kokarinta na wanzar da zaman lafiya a sassan kasar da kuma kiyaye hadin kan kasa.
Duk da haka, shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata sojin kasar su bi horarwar da suka samu na mutunta hakkin bil'adama a lokacin da ake takalar su.