Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya tafi bikin Sallah a Daura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah.
Hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta sun nuna manyan jami'an gwamnati da Sarakuna suna tarbar shugaban kasar.
Cikin wadanda suka tarbe shi har da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sarakunan Katsina da Daura.
A ranar 19 ga watan nan ne Shugaba Buhari ya koma Najeriya, bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a birnin London.