Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Niger: Manoma da makiyaya na samun horo kan zaman lafiya
Rikici tsakanin manoma da makiyaya abu ne mai tsohon tarihi a Jumhuriyar Niger.
Tun shekaru da dama da suka gabata, tashin hankali tsakanin bangarorin biyu ya kasance tamkar ruwan dare a yankunan karkara.
Lamarin fada tsakanin manoma da makiyaya yafi gudana ne a a lokacin damuna.
A mafi yawan lokuta barnar da ake cewa dabbobin makiyaya na yi a gonakin manoma da mayar da wurin kiwo gona da dai sauran su, na daga cikin ire-iren abubuwan da ke haddasa rikicin.
Shi dai irin wannan rikici da zarar ya wakana sai an samu asarar rayuka da dukiya.
Ganin irin dumbin asarar rayuka da dukiya da ake samu sanadiyar irin wannan rikice-rikice na jahilci a kasar ta Niger, yanzu haka a jihar Damagaram da ke gabas masu kudanci da kuma ta kasance wani yankin da al'ummomin biyu ke zaune a tsakanin su , na bayar da horo ga bangarorin biyu ta yadda za su zauna da juna lafiya.
Wata kungiya ce mai suna FENAP ta shirya wannan bayar da horon da nufin taimaka wa bangarorin fahimtar juna, abun da ya gagara shekara da shekaru a tsakaninsu.
Noma da kiwo sun kasance manya-manyan hanyoyin samar da arziki a kasar ta jumhuriyar Niger.