Kun san abin da ya sa Larabawa suka yi wa Qatar taron-dangi?

Saudiyya da Bahrain da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa da Masar sun katse hulɗar diplomasiyya da Qatar, kan zargin mara wa ta'addanci baya.

Wannan sanarwa ta biyo bayan ƙaruwar tunzurin da ke akwai a yankin, tun bayan zargin kutsen da aka yi wa kamfanin dillancin labaran ƙasar Qatar a cikin watan jiya.

Bahrain dai yi ƙorafin cewa Qatar na yi mata katsalandan a harkokin cikin gida.

Yayin da ita ma, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zargi Qatar da yunƙurin wargaza tsaro a yankin Gulf.