An dakatar da jami'in FRSC kan yi wa mata askin dole

An dakatar da Kwamandan hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC na jihar Rivers, sakamakon samun sa da laifin yankewa wasu jam'ian hukumar mata gashinsu.

Shugaban hukumar Boboye Oyeyemi ne ya bayar da izinin dakatar da Mista Andrew A. Kumapayi tare da matan da ya yankewa gashin nasu, don a gudanar da bincike kan lamarin.

Rahotanni sun ce matan sun sanya dogon gashi ne sun kuma fitar da shi a harabar hukumar da ke birnin Fatakwal, wanda hakan ya sabawa ka'idar aikin.

Shugaban hukumar Mista Boboye ya yi Allah-wa-dai da hotunan da suke ta yawo a shafukan sada zumunta wadanda suke nuna Mista Kumapayi yana yanke gashin jami'ai matan.

Tun a ranar Litinin da yamma ne hotunan yadda Mista Kumapayi ya sa almakashi yana yanke wa matan gashi suka fara bazuwa a shafukan sada zumuntar, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar, inda da yawan mutane ke tir da halin Kwamandan, yayin da kalilan kuwa suna ganin laifin matan ne.

Wasu da dama sun yi ta zagin sa suna kiran sa da sunaye suna kuma yi masa kallon wanda bai san darajar mata ba.

Mista Kumapayi ya aikata wannan abu ne yayin da jami'an ke fareti da safiyar Litinin, shi kuma yana zagawa don ganin abin da ke wakana.