Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kifewar kwale-kwale ta janyo wa wasu ɗauri a Masar
Wata kotu a Masar ta yanke wa mutum 56 hukuncin dauri saboda samunsu da hannu a kifewar da wani kwale-kwale ya yi a watan Satumba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 200.
An yanke wa mutanen hukuncin daurin shekara 14 bayan an same su da laifin kisan kai da yin sakaci.
Kwale-kwalen na kan hanyarsa ta zuwa Italiya ne lokacin da ya kife a nisan kilimita 12 daga tekun da ke birnin Rosetta da ke gabar teku.
An yi kiyasin cewa kusan mutum 450 ne a cikin kwale-kwalen, cikin su har da kusan mutum 100 da aka sanya a wurin zaman direba.
Mutum 163 suka tsira daga kwale-kwalen, kuma akasarinsu 'yan kasar ta Masar ne.
Akwai 'yan kasashen gudu hijirar Syria da Eritrea da kuma Somalia a cikin kwale-kwalen.