Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kun taba jin daya daga cikin hirarrakin da Ahmadu Bello ya yi da BBC?
To a ci gaba da kawo muku jerin rahotanni da hirarraki dangane da cikar sashen Hausa na BBC shekaru 60, ga wani bangare na hirar da sashen ya taba yi da Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.
A ranar 2 ga watan Agusta na shekarar 1960, Umaru Dikko - wato mutum na biyu da ya fara aiki a sashen Hausa na BBC - ya yi wata hira da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, inda aka tambaye shi dalilin ziyarar da ya kai Birtaniya a wancan lokaci.
Sardaunan ya yi bayani kan dalilin ziyarar da kuma wani na batu na neman taimako daga kasashen Turai.
Ga dai kadan daga cikin hirar: