Trump ya yi babbar kasada shiga yaƙin Iran da Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Donald Trump, shugaban da ya sake komawa Fadar Gwamnatin Amurka (White House ) a watan Janairu da alƙawarin zama mai wanzar da zaman lafiya, abin mamaki ya jefa ƙasarsa cikin yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.
Saɓanin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da ya sake komawa kan mulki, Trump a yanzu na jagorantar yankin da ke dab da rincaɓewa da yaƙi fiye da, a baya - yaƙin da ita kanta Amurka ke da hannu dumu-dumu a ciki.
A wani jawabi da ya yi ga al'ummar ƙasar daga Fadar Gwamnatin (White House), sa'a biyu bayan da ya sanar a shafinsa na intanet cewa sojojin Amurka sun kai hari kan cibiyoyin nukiliya uku a Iran, shugaban na Amurka ya ce, an yi gagarumar nasara a harin.
Shugaban ya bayyana fatan cewa matakin nasa zai bayar da damar samun dawwamammen zaman lafiya- inda Iran ba ta da sauran wani ƙarfi ko dama ta zama mai makamin nukiliya.
Sai dai kuma a nata ɓangaren Iran ta ce wannan hari da Amurka ta kai mata illa ƴar kaɗan ya yi wa tashar ta nukiliya ta Fordo mai tsananin tsaro.
A yanzu dai ba wanda ya san gaskiyar lamarin - sai dai kamar yadda ƴan magana kan ce lokaci alƙali - nan gaba gaskiyar lamarin za ta bayyana.
Trump wanda yake kewaye hagu da dama da manyan ƙusoshin gwamnatinsa - Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance, da Sakataren harkokin waje Marco Rubio, da kuma Sakataren harkokin tsaro Pete Hegseth, ya gargaɗi Iran cewa idan ba ta yi watsi da shirinta na nukiliya ba, za ta fuskanci wasu munanan hare-hare a nan fiye da wanda ta gani a yanzu.
Duk da wannan tunƙaho da jijji da kai da fankama da shugaban yake nunawa ci gaba da shiga wannan rikici ta kai hare-hare a Iran zai iya kasancewa wani mummunan abu ga Amurka da yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargaɗin samun tashe-tashen hankali a dalilin shigar Amurka wannan rikici kai tsaye, yana cewa dama tuni yankin yana dab da faɗawa rikici.
Idan Iran ta rama kamar yadda Ayatollah Ali Khamenei ya yi gargaɗin cewa idan Amurka ta kai wa ƙasarsa hari to, hakan kuma zai ƙara sa Amurka ta ƙara martani.
Wa'adin mako biyu ya zama kwana biyu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Furucin da Trump ya yi a makon nan cewa dole ne Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba, ya tura shugaban inda yake da wuya ya iya dawowa baya. Ita ma Iran da irin barazanar da take yi ta sa nata a irin wannan matsayi.
Mai kaya ya rantse ɓarawo ya rantse - yadda husuma a nan za mu ce yaƙi yake farawa ke nan - daga nan kuma sai abin da hali ya yi domin zai yi ta girma har ma ya fi ƙarfin tunani da ikon waɗanda suka janyo shi.
A ranar Alhamis, Donald Trump, ya ba wa gwamnatin Iran wa'adin mako biyu kafin ya yanke shawara kan ko ƙasarsa za ta shiga yakin kai tsaye ko kuma a'a, to amma sai ya yi gajen haƙuri, ya ƙosa da kwana biyu kawai.
A ranar Asabar da daddare shugaban na Amurka ya sanar da cewa Amurka ta ɗauki mataki.
To me ya janyo wannan?
Daman maganar wa'adin mako biyun yaudara ce? Ko yunƙuri ne na yaudarar Iraniyawa su saki jikinsu a cikin waɗannan kwanaki? Ko tattaunawar da ake yi ta bayan gida ce ƙarƙashin jagorancin mutumin da Trump ya zaɓa domin jagorantar tabbatar da zaman lafiya Steve Witkoff ce ta wargaje?
Ba dai wani cikakken abu da aka sani bayan kai harin. To amma a shafinsa na sada zumunta da muhawara da kuma jawabinsa da aka yaɗa, Trump ya nuna aniyarsa ta neman zaman lafiya.
Ƙila a iya cewa da gaske yake da hakan. Yayin da Isra'ila ke ta ƙoƙarin ganin ta kassara ƙarfin sojin Iran, har yanzu ƙasar ta Ayatollah, tana da tarin makamai.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba yaƙin zai iya rincaɓewa
A yanzu dai an zuba ido a ga salon da yaƙin zai ɗauka tun da Amurka ta shiga yaƙin kai tsaye da wanan hari da ta kai wa Iran.
Ta yaya, kowane irin martani Iran za ta yi kan wannan hari da Amurka ta kai wa cibiyoyinta na nukiliya uku ciki har da Fordo wadda take cike da buri da tunƙaho a kanta?
Trump na fatan ganin harin zai tilasta wa Iran ta sassauto sosai a yayin zaman yarjejeniya, to amma ga alama abu ne mawuyaci a ce ƙasar da ba ta da niyyar magana a lokacin da Isra'ila ke kai mata hare-hare a ce ta miƙa wuya yayin da Amurka ta fara kai mata hari da kanta ita ma.
Kuma yayin da Trump ke nuna alamun cewa harin na Amurka sili-ɗaya-ƙwale, wanda kuma ya yi nasar, idan ya kasance saɓanin haka, to shugaban zai shiga cikin matsi na ganin an ƙara kai hare-haren, ko kuma a ce shugaban ya yi babban kasada ta siyasa domin ƴar riba kaɗan ta soji.
Shugaban da ke iƙirarin zaman lafiya ya yi kasadar siyasa
Haɗarin ya haɗa da damuwa ta siyasa ta cikin gida tare da batutuwa na tsaro na duniya.
Tuni batun harin na Amurka a kan Iran ya gamu da kakkausar suka ba daga ɓangaren ƴan hamayya ba kaɗai na Democrat, har ma daga cikin masu ra'ayin Trump na fifita Amurka (America First).
Yanayin yadda shugaban ya gabatar da jawabinsa ga ƙasa hagu da damansa manyan masu ba shi shawara uku na kusa da shi, kamar wani yunƙuri ne na nuna haɗin-kai a cikin jam'iyyarsa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Vance, musamman ya yi fice wajen ganin Amurka ta taƙaita manufofinta na waje - ta fi bayar da fifiko a kan kanta.
Kuma ko a baya-bayan nan Mista Vance ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa Trump har yanzu ba shugaba ne mai katsalandan ba, wanda kuma ya ce ya kamata magoya bayansa su yarda da hakan.
To idan ya kasance wannan harin shi ne ɗaya kawai na Amurka a kan Iran, Trump zai iya tsira daga rarrabuwar kan da ke cikin mabiyansa.
Amma kuma idan har harin ya kai ta ga tsunduma ga yaƙin shugaban zai iya gamuwa da tawaye daga cikin mabiyansa.
Harin na ranar Asabar, tsattsauran mataki ne ga shugaban da ya bugi ƙirji a jawabinsa na farko a matsayin shugaba da cewa shi ba zai janyo wasu sababbin yaƙe-yaƙe ba.
Kuma musamman ma ganin yadda a lokacin yaƙin neman zaɓensa a shekarar da ta wuce, ya riƙa sukar shugabannin Amurka da suka gabace shi, waɗanda suka shigar da ƙasar wasu rikice-rikice na waje.
Yanzu dai Trump ya yi nasa, amma kuma abin da zai iya biyo baya daga yanzu abu ne da ba shi da iko kusan gaba-ɗaya a kai.










