Abin da muka sani kan hare-haren da Amurka ta kai a cikin Iran

Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 8

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce jiragen yaƙin Amurka sun jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lamarin da ya ƙara girman yaƙin da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran.

"Ku sani cewa akwai sauran wurare da dama da ake son kai wa hari. A wannan dare (mun kai hari ne) kan wurin da ya fi wahala kuma mafi hatsari," in ji shugaban na Amurka a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi ga al'ummar ƙasar.

"Amma idan aka kasa dawo da zaman lafiya cikin sauri za mu je kan sauran wuraren da muke hari cikin gaggawa da ƙwarewa ba tare da kuskure ba."

Ɗaya daga cikin cibiyoyin da aka kai wa harin ita ce Fordo, wata cibiyar inganta makamashin uraniun wadda ke ɓoye a ƙarƙashin ƙasa, wadda kuma ke da matuƙar muhimmanci ga shirin nukiliyar Iran.

Ya zuwa yanzu ba mu san irin ɓarnar da harin na Amurka ya yi wa cibiyar ba.

Isra'ila ta ce ita da Amurka ne suka shirya kaf, yadda aka kai hare-haren.

Amurka ta tuntuɓi Iran ta hanyar diflomasiyya a ranar Asabar, inda ta shaida wa Iran ɗin cewa hare-haren sama kawai za ta ƙaddamar, kuma ba su da alaƙa da "yunƙurin sauya gwamnati", kamar yadda wasu jami'an gwamnatin Amurka suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS, wadda BBC ke haɗin gwiwa da ita.

Iran za ta iya mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hari kan kadarorin Amurka da ke yankin. Jami'an gwamnatin Iran sun sha gargaɗin Amurka cewa shigan ta cikin yaƙin zai iya dagula al'amura tare da haifar da yaƙi a faɗin yankin, kuma tabbas za su mayar da martani.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi allawadai da hare-haren na Amurka inda Antonio Guterres ya ce babbar bazarana ce ga zaman lafiyar duniya kuma mataki ne mai hatsari na kara rura wutar yaki, haka ma kasashe aminan Iran irinsu Cuba da Venezuela sun yi allawadai da hare-haren.

Ga abin da muka sani ya zuwa yanzu game da hare-haren.

Waɗanne wurare Amurka ta kai wa hari kuma da waɗanne makamai ne?

Jiragen yaƙin Amurka sun jefa bam kan cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran
Bayanan hoto, Jiragen yaƙin Amurka sun jefa bam kan cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amurka ta ce ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya uku – Fordo da Natanz da kuma Isfahan.

An yi amannar cewa cibiyar nukiliyar Iran ta Fordo na a wani wuri ne mai yawan tuddai da ke kudancin Tehran, kuma an yi amannar cewa tana ɓoye ne a can ƙarƙashin ƙasa.

Zurfin da cibiyar nukiliyar ke da shi a ƙarƙashin ƙasa ya sanya makaman Isra'ila ba za su iya kaiwa inda za su lalata ta ba. Inda aka yi amannar cewa bam ɗin Amurka da ake kira "bunker buster" shi kaɗai ne zai iya lalata cibiyar.

Ana kiran bam ɗin GBU-57. Yana da nauyin kilogiram 13,000, kuma yana iya ketawa ta cikin kankare mai zurfin mita 18 ko kuma tudun ƙasa mai zurfin mita 60 kafin ya tarwatse, in ji masana.

An tabbatar da cewa cibiyar Fordo tana da zurfin mita 80 zuwa 90 a ƙarƙashin ƙasa, saboda haka babu tabbas kan cewa bam ɗin na Amurka zai iya tarwatsa ta, sai dai shi kaɗai ne ake ganin zai iya yunƙurin yin hakan.

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ce an yi amfani ne da bam ɗin na GBU-57.

Wace ɓarna hare-haren suka yi wa Iran?

Babu tabbas tukuna kan illar da hare-haren na Amurka suka yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran, haka nan babu tabbas ko akwai mutanen da abin ya rutsa da su.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran ta ce jefa wa cibiyoyin nukiliyarta bam "gagarumin saɓa" dokar ƙasashen duniya ne.

Saudiyya da hukumar sanya ido kan makamin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce ba a samu ƙaruwar yaɗuwar sanadari mai illa ga ɗan'adam ba bayan kai harin.

Mataimakin daraktan shirye-shiryen siyasa na kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran, Hassan Abedini ya ce Iran ta kwashe mutane daga waɗannan cibiyoyin nukilyar "kafin kai harin".

A lokacin da ya bayyana a kafar talabijin ta gwamnatin, ya ce "ba a yi wata babbar ɓarna ga Iran ba domin an riga an kwashe kaya daga wuraren".

A cikin jawabinsa ta kafar talabijin, Trump ya ce "an lalata baki ɗaya cibiyoyin nukiliyarta".

To amma a lokacin da ya tattauna da BBC, wani tsohon mataimakin sakataren harkon wajen Amurka kan siyasa da harkar soji, Mark Kimmit ya yi ɗan shakku kaɗan game da hakan.

"Babu yadda za a yi a ce an lalata su baki ɗaya," in ji shi.

Iran ta ce sama da mutum 200 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar rikici na baya-bayan nan tsakaninta da Isra'ila, kuma sama da mutum 1,200 ne aka jikkata.

A ɓangare ɗaya Isra'ila na ta ƙarfafa tsaronta yayin da Amurkar ta kai waɗannan hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Yanzu haka hukumomi a Isra'ilar ta ɗauki wasu matakai kan tsaro, ciki har da "haramta ayyukan bayar da ilimi, da taruka da kuma zuwa aiki" – bayan hare-haren da Amurkar ta kai wa Iran.

Ta yaya Iran za ta iya mayar da martani?

Ƙarfin sojin Iran ya ragu sanadiyyar hare-haren da Isra'ila ta kai wa cibiyoyin sojinta a baya-bayan nan, kamar yadda masana suka faɗi, haka nan kuma an tarwatsa ƙungiyoyin da ke taimaka wa Iran, kamar Hezbollah a Lebanon da Syria da kuma Hamas a Gaza.

To sai dai har yanzu Iran na da ƙarfin yi wa abokan adawarta ɓarna.

Jami'an gwamnatin Iran sun gargaɗi Amurka da kada ta tsoma kanta cikin rikicin, inda suka ce za ta fuskanci "ɓarnar da ba za ta gyaru ba" kuma akwai hatsarin jefa ɗaukacin yankin cikin yaƙi.

Iran ta yi barazanar kai hari kan sansanonin Amurka da ke yankin.

Wakilin BBC kan tsaro Frank Gardner ya ce a yanzu dole ne Iran tana da zaɓi uku kan yadda za ta mayar da martani game da harin da Amurkar ta kai mata:

  • Kada ta yi komai: Wannan zai iya sanyawa Amurka ta tsagaita daga kai mata ƙarin hare-hare. Za kuma ta iya komawa kan teburin diflomasiyya tare da komawa tattaunawa da Amurka. To amma ƙin yin wani abu zai nuna cewa gwamnatin Iran tana da rauni, musamman bayan gargaɗin da ta yi na ɗaukar matakai idan Amurka ta kai mata hari. Ƙila za ta ga cewa cigaba da kare goyon bayan da take samu daga al'ummarta ya fi muhimmanci a kan yin abin da zai sa kada Amurka ta ci gaba da kai mata hari.
  • Mayar da martani mai tsanani cikin sauri: Har yanzu Iran na da tarin miyagun makamai masu linzami waɗanda ta daɗe tana haɗawa tana tarawa a tsawon shekaru. Akwai sansanonin sojin Amurka kimanin 20 a faɗin Gabas ta Tsakiya da za ta iya kai wa hari. Za ta kuma iya ƙaddamar da harin jirage marasa matuƙa kan jiragen ruwa na yaƙi na Amurka.
  • Jinkirta mayar da martani: Wannan na nufin Iran za ta iya dakatawa har sai hankula sun lafa daga nan sai ta ƙaddamar da hare-haren ba-zata kan sansanonin Amurka a lokacin da suka sassauta matakan tsaronsu.

Amurka tana da sansanonin sojinta a wurare aƙalla 19 da ke yankin na Gabas ta Tsakiya, cikin har da waɗanda ke ƙasashen Bahrain da Masar da Iraqi da Kuwait da Qatar da Saudiyya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Wani sansani da ake ganin zai fi wa Iran sauƙin kai wa hari shi ne babban sansanin sojin ruwa na Amurka da ke Mina Salman a ƙasar Bahrain.

Iran kuma za ta iya toshe mashigar Hormuz - ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafiya muhimmanci a duniya – wanda ya haɗa Persian Gulf da tekun Indiya.

Ta wannan mashiga ce ake safarar kashi 30 cikin ɗari na man fetur da ake amfani da shi a duniya.

Haka nan Iran za ta iya kai hari kan wasu hanyoyin sufurin ruwa da za su iya haifar da matsala a kasuwannin duniya.

Iran za ta kuma iya kai hari kan kadarorin da ke kusa da ita na ƙasashen da take ganin suna taimaka wa Amurka, lamarin da zai iya sanyawa yaƙin ya faɗaɗa a yankin.

Jim kaɗan bayan harin da Amurka ta kai wa Iran, ƙasar ta sake harba wasu jerin makamai masu linzami zuwa Isra'ila.

An ji fashewar abubuwa a biranen Haifa da Tel Aviv da kuma Jerusalem.

Yadda abin ya samo asali

A ranar 13 ga watan Yuni ne Isra'ila ta ƙaddamar da hari kan cibiyoyin nukiliya da na sojin Iran da dama. Ta ce ta yi hakan ne domin kawar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya, bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa Iran na dab da mallakar makamin.

Iran ta dage kan cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne. A matsayin martani, Iran ta ta ƙaddamar da hare-haren ɗaruruwan makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa kan Isra'ila.

Tun daga wancan lokacin ne ƙasashen biyu suka ci gaba da musayar wuta ta sama, tsawon sama da mako ɗaya.

Trump ya daɗe yana cewa ba ya ƙaunar Iran ta mallaki makamin nukiliya. Bayanai na tabbatar da cewa Isra'ila ta mallaki makamin nukiliya, sai dai ba ta taɓa tabbatarwa ko kuma musanta batun ba.

A watan Maris, shugabar hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka, Tulsi Gabbard ta ce duk da cewa Iran ta ƙara ingantawa da kuma yawan makamashin Uranium ɗinta sosai, amma ba ta fara batun samar da makamin nukiliya ba – wani abu da Trump ya ƙaryata a baya-bayan nan, ya ce "ba haka ba ne".

A lokacin yaƙin neman zaɓensa Trump ya soki gwamnatin Amurka da ta gabata, inda ya ce ta shiga cikin "yaƙe-yaƙe na babu gaira babu dalili waɗanda ba za su ƙare ba" a Gabas ta Tsakiya, kuma ya ci alwashin janye Amurka daga duk wasu rikice-rikice na ƙasashen duniya.

Amurka da Iran na kan tattaunawa game da nukiliya a lokacin da Isra'ila ta ƙaddamar da harin.

Bayan haka sai Trump ya bai wa Iran wa'adin mako biyu na ganin ta shiga yarjejeniya kafin ya yanke hukuncin kai mata farmaki – sai dai ba a je ko ina game da wannan wa'adi ba.

Ko Trump na buƙatar amincewar Majalisa kafin shiga yaƙi?

A ƙarƙashin dokokin Amurka, shugaban ƙasa - shi kaɗai - ba ya da ikon ayyana yaƙi kan wata ƙasa a hukumance.

Majalisar dokoki – wadda ta ƙunshi zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai da na dattijai – ne kawai suke da ƙarfin yin hakan.

To amma doka ta ce shugaban ƙasa shi ne shugaban dakarun ƙasar. Wanda hakan ke nufin zai iya tura sojoji su kai hari a wani wuri ba tare da ayyana yaƙi a hukumance ba.

Misali, matakin Trump na ƙaddamar da hare-hare ta sama kan gwamnatin shugaba Assad a Syria cikin shekarar 2017, bai buƙaci amincewar majalisar dokoki ba. A madadin hakan, Trump ya yi gaban kansa ne kawai, inda ya kafa hujja da buƙatar tsaron ƙasa.

A baya-bayan nan wasu ƴan majalisar dokokin Amurka daga ɓangarorin biyu sun yi yunƙurin taƙaita ƙarfin Trump na kai wa Iran hari ta hanyar tura wani ƙudurin ikon ayyana yaƙi a Majalisar wakilai.

Sai dai za iya shafe makonni kafin a kaɗa ƙuri'a kan batun, sannan kuma a mafi yawan lokuta irin waɗannan dokoki suna kasancewa ne kawai a rubuce.