Ko yaƙin Isra'ila zai tursasa wa Iraniyawa yin kaura zuwa Turkiyya?

Asalin hoton, OZAN KÖSE/AFP/GETTY IMAGES
Rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran, wanda ya barke a ranar 13 ga watan Yuni ya haifar da fargabar kwararan ‘yan gudun hijira masu dimbin yawa daga Iran zuwa Turkiyya.
Idan aka tuna da abin da ya faru na tarwatsewar al’umma a lokacin yakin basasan Syria, wasu na cewa kila abin da zai faru ke nan game da rikicin Iran da Isra’ila.
Sai dai ya zuwa yanzu dukkanin kafafen yada labarai da sashen BBC mai yada labari da harshen Turkanci ya tattauna da su, sun nuna cewa ba a fara samun tudadar ‘yan gudun hijira masu yawa ba tukuna.
Hukumar kula da kaura ta Turkiyya ta mayar da martani game da labarin kamfanin dillanci labarai na Anadolu, tana mai cewa ikirarin cewa akwai kwararan ‘yan gudun hijira a yanzu haka daga Iran zuwa Turkiyya ”karya ce tsagwaron ta”.
Wasu masharhanta da BBC ta tattauna da su sun ba su tunanin za a samu kwararan ‘yan gudun hijira masu yawa a halin da ake ciki a yanzu.
Sun ce za a iya samun tarwatsewar al’umma ne idan yakin ya kazance ko kuma aka samu tarzoma a cikin gida.
Sai dai sun ce duk da haka nan za a samu bambanci tsakanin yadda aka samu kwararan mutane daga Syria da kuma yadda za a samu daga Iran.
Akwai cibiyoyin tsallaka iyaka uku da ake amfani da su kan iyakar Iran da Turkiyya ta kasa: Bazargan, Razi da kuma Sarv. Sannan kuma akwai layin jirgin kasa na Razi da ke aiki.
Yanzu haka zirga-zirgar da aka gani ta kan iyakar kawai ita ce ta Iraniya da suke kokarin komawa gida daga Turkiyya.
Shugaban cibiyar nazarin bayar da mafaka da kuma kaura, Metin Çorabatir, ya yi amannar cewa “ya zuwa yanzu ba mu ga wata aniya daga Iraniyawa ta barin kasarsu ba.
Abin ma da aka gani shi ne Iraniyawan da suka zo Turkiyya domin kasuwanci ko yawon bude ido ko kuma neman lafiya suna ta komawa ne gida ta iyakar Van, bayan da aka rufe sararin samaniya. Suna ta kokarin komawa Iran ta amfani da motocin bas, daboda haka abin da ake samu shi ne tudadar mutane daga Turkiyya zuwa Iran.“

Asalin hoton, Milli Savunma Bakanlığı
Sashen harshen Persia na BBC ya ce ana ganin dalilai biyu ne suka sanya duk da cewa Iraniya suka ki kwarara zuwa Turkiyya duk da cewa akwai yarjejeniyar cewa yan kasashen biyu za su iya shiga makwafciyarsu ba tare da takardar biza ba.
Na farko shi ne karancin man fetur da kuma cunkoson motoci a manyan biranen Iran ya sanya al’umma sun kasa kwarara zuwa kan iyaka da Tirkiyya.
Na biyu shi ne Iraniyawa da dama sun yi amannar cewa yakin ba zai dade ba, kuma akwai yiwuwar za a samu malaha nan ba da dadewa ba.
Mutanen Iran za su iya shiga Turkiyya su zauna har kwana 90 ba tare da sai suna da takardar biza ba.
Dr. Didim Danish, na Jami’ar Galatasaray ya ce za a iya samun Iraniyawan da za au taallaka zuwa Turkiyya domin kare kai.
Sai dai ya ce “a yanzu ba na tunanin cewa mutane da yawa za su gudu zuwa Turkiyya ko kuma ya zama wata matsala ta ‘yan gudun hijira da za ta dade.”

Asalin hoton, MINA/MIDDLE EAST IMAGES/GETTY IMAGES
Me zai faru idan yakin ya tsananta?
Masana na ganin cewa za a iya samun lokacin da Iraniyawa da dama za su fice daga kasar.
Shugaban cibiyar bincike kan bayar da mafaka da kaura, Metin Çorabatir ya ce yin kauarar Iraniya ya dogara ne da abu biyu.
“Idan yakin ya tsananta har ya kai ga ana jefa bama-banau a unguwanin al’umma a cikin birane.
Haka nan maa, idan aka fara tattaunawar sulhu amma sai gwamnatin kasar ta juya akalarta zuwa kamurran cikin gida, kamar kamenal’umma na gobe. Wannan zai sanya mutane su nemi tserewa daga kasar.
To amma ficewar dimbin al’umma daga kasar ta Iran ya danganta ne da yadda yakin ya kasance.”

Asalin hoton, CHRIS MCGRATH/GETTY IMAGES
Baya ga Turkiyya, Iran tana kuma hada iyaka da kasashen wasu kasashe biyar, wato Azerbaijan da Armenia da Turkministan, da Afghanistan da kuma Pakistan.
"Tsarin rayuwa da al’adar Iraniya ta sha bamban”

Asalin hoton, CEMA YURTTAŞ/DIA IMAGES/GETTY IMAGES
Yayin da ake ci gaba da muhawar kan batun man tudadar Iraniyawa zuwa cikin Turkiyya, ana kwatanta lamarin da abubuwan da suka faru a lokacin yakin Syria da Afgahnistan da kuma ‘yan irin wadannan kasashe da ke zaune a Turkiyya.
Akwai doguwar muhawara da ake yi a Turkiyya kan yadda za a shigar da su tsarin rayuwa ta Turkawa.
Farfesa Dr. Aysen ya bayyana cewa akwai bambanci ta tsarin rayuwa da al’ada tsakanin Iraniyawa da kuma mutanen Syria.
“Mutanen Iran da suka yi kaura zuwa Turkiyya, idan aka kwatanta su da na Syria da Afghanistan da ma Pakistan, za a ga cewa mafi yawancinsu masu ilimi ne. Duk da cewa ana kallon su Iraniyawa ne amma wasu daga cikinsu Azeei ne. Wadannan mutane sukan saje da al’adun Turkawa cikin sauki savoda nakaltar harshen da kuma kusantakarsu da Turkiyya.






