Wane martani Iran za ta mayar bayan harin Amurka?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Jo Floto
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East bureau chief
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 3
Da Benjamin Netanyahu ya fito domin jawabi game da halin da ake ciki a game da yaƙin da suke yi da Iran a ofishinsa na firaminista a safiyar yau, an riga an samu labarin harin Amurka da ya kawo sauyi dangane da yaƙin.
Ya yi jawabin ne da Ingilishi, inda ya fito ƙarara ya yaba wa Amurka da shugabanta Donald Trump bisa ɗaukar matakin kai hari a sansanonin nukiliyar Iran.
Maganar Netanyahu ta kasance cike da farin ciki, musamman ganin a tsawon lokacin da ya yi yana harkokin siyasa, ya kasance cikin yawan nanata maganar barazanar da Isra'ila ke fuskanta daga Iran.
A cikin kimanin shekara 15 da suka gabata, Netanyahu ya kasance cikin neman ƙawar ƙasarsa Amurka tare da fahimtar da ita cewa yaƙi ne kawai (kuma makaman Amurka ne kawai) zai iya tarwatsa shirin nukiliya na Iran.
A daidai lokacin da yake yaba matakin da Trump ya ɗauka, wanda ya ce, "zai kawo sauyi," shi ma Netanyahu zai iya yaba wa kansa bisa ƙoƙarin da ya yi wajen canja ra'ayin Amurka da shugabanta, wanda ya yi yaƙin zaɓe da cewa ba zai shiga yaƙin da babu ruwan Amurka ba, kuma yake da magoya bayan da ba sa ƙaunar Amurka ta shiga yaƙin Iran.
Haka kuma jami'an leƙen asirin Amurka ba su bayyana rahoton bincikensu game da hali ko matakin da Iran ke ciki na makamin nukiliya ba.
Tun farkon yaƙin, wanda aka fara kimanin kwana 10 da suka gabata, sojojin Isra'ila sun sha nanata cewa za su iya magance barazanar da suke fuskanta daga Iran ba tare da neman taimako ba.
Amma a bayyane yake cewa Amurka ce kaɗai ke da makaman da ake buƙata domin tarwatsa cibiyar makamin nukiliyar Iran ta Fordo, wadda aka gina a cikin duwatsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan har harin da aka kai jiya sun tarwatsa cibiyoyin nukiliyar, to lallai Netanyahu zai iya cewa burinsa na ƙaddamar da yaƙin run farko ya cika, wanda kuma zai iya kawo ƙarshen yaƙin. Amma a nata ɓangaren, Iran ta ce ta riga ta kwashe kayayyakin aikin sarrafa makamin zuwa wasu wuraren daban.
Amma ba don harin na daren jiya ba, da Isra'ila ta cigaba da ƙaddamar da hare-hare a cibiyoyin da ta yi shekaru yana tattarawa.
Da ta cigaba da kai hare-haren kan sojojin Iran da kwamandojita da masana nukiliyarta da wasu kadarorin gwamnatin ƙasar.
Lallai bama-baman B2 sun kawo sauyi a yaƙin, amma faɗaɗar yaƙin, na ta'allaƙa ne da yadda Iran da ƙawayenta suka mayar da martani.
A makon jiya, jagoran addinin Iran ya ɗauki alwashin mayar da martani idan Amurka ta shiga yaƙin.
A ranar Asabar da ta gabata, ƴan Houthi da ke Yemen - ƙungiyar da ke ƙawance da Iran - ta yi barazanar kai hari kan jiragen Amurka da suke wucewa ta tekun Red Sea idan ƙasar ta shiga yaƙin.
Yanzu sojojin Amurka da ƴankasuwa da sauran Amurkawa da ke yankin suna cikin haɗari. Iran za ta iya mayar da martani ta hanyoyi da dama, ciki har da kai hari kan jiragen ruwan Amurka da sansanonin sojinta da ke yankin gabas ta tsakiya da ma kawo tsaiko a dakon man fetur daga yankin, wanda hakan zai sa farashin man ya yi tashin gwauron zabi.
Yanzu dai Amurka ta ce ta kammala aikin soji, kuma ba ta da burin kawo sauyin gwamnati a Iran.
Wannan zai sa Iran ta sassauta irin martanin da za ta mayar, wataƙila sai dai ta mayar da martanin ta yadda ba za ta yi illa sosai ga Amurka ba, ko kuma ta mayar da martanin ta bayan fage.
Yanzu dai kusan kowa a yankin gabas ta tsakiya na jiran ganin abin da zai faru ne - jiran ganin ko yaƙin ya zo ƙarshe ne, ko kuma harin ya buɗe sabon babi ne yaƙin.










