Yadda masu kutse suka yi fashin kirifto mafi girma a tarihi

Lokacin karatu: Minti 4

Masu kutse da ake tsammanin ma'aikatan gwamnatin Koriya ta Arewa ne sun canza kuɗin da ya kai dala miliyan 300 cikin dala biliyan 1.5 da suka sata na kuɗin crypto zuwa aljihunsu.

Miyagun da aka fi sani da Lazarus Goup sun wawashe damman kuɗaɗen intanet ɗin ne yayin wani kutse kan dandalin canza kuɗin crypto na Bybit mako biyu da suka gabata.

Tun daga lokacin ne kuma ake ta kair ruwa rana wajen ganowa da hana masu kutsen canza kuɗaɗen zuwa garin kuɗin da za su iya amfani da shi.

Ƙwararru na cewa gungun masu kutsen kan yi aiki tsawon awa 24 a kullum - inda suke tura su asusun ayyukan gwamnatin ƙasar.

"Masu kutsen na amfani da kowane minti ɗaya yayin da suke yunƙurin ɓatar da sawunsu, kuma suna da ƙwarewa matuƙa a harkokinsu," a cewar Dr Tom Robinson, ɗaya cikin masu dandalin bin sawun 'yan crypto mai suna Elliptic.

Daga cikin dukkan miyagu a harkar crypto, Koriya ta Arewa ta fi kowacce ƙwarewa wajen halsta kuɗin haram, kamar yadda Dr Robinson ya yi bayani.

"Da alama ɗaki guda gare su na mutanen da yin wannan aiki ta hanyar amfani da na'urorin da ke sarrafa kansu. Muna iya ganin yadda suke ɗaukar hutun 'yan awanni kacal a duk rana, ƙila rukuni-rukuni domin ci gaba da canza kuɗaɗen."

Nazarin da Elliptic ya yi ya daidai da na Bybit, wanda ya ce kashi 20 cikin 100 na kuɗin "sun ɓuya", abin da ke nufin da wuya a iya ƙwato su.

Amurka da ƙawayenta na zargin Koriya ta Arewa da kai harin kutse a 'yan shekarun nan domin taimaka wa gwamnatin ƙasar wajen samar da makaman yaƙi ciki har da nukiliya.

A ranar 21 ga watan Fabrairu, miyagu suka kutsa shafin ɗaya daga cikin masu hada-hada a ByBit da zimmar sauya adireshin asusunsa (wallet) inda ake tura kuɗin Ethereum 401,000.

ByBit ya yi tunanin yana tura kuɗin ne zuwa asusunsa, ashe maharan yake turawa gaba ɗaya.

Ben Zhou, shugaban dandalin na ByBit ya tabbatar wa kwastomomi cewa ba a ɗauki ko ƙwandalarsu ba.

Kamfanin ya maye gurbin kuɗaɗen da na rance daga masu zuba jarinsa, amma ya ce "sun ayyana yaƙi da Lazarus".

Shirin bayar da lada na ByBit na ƙarfafa wa mutane gwiwa domin bin sawun kuɗin, da kuma daskarar da su idan zai yiwu.

Akan wallafa duka cinikayyar da aka yi ta kuɗin crypto a kan dandalin da jama'a za su gani, saboda haka za a iya bin sawun kuɗin yayin daLazarus ke tuttura su wuri-wuri.

Idan maharan suka yi yunƙurin yin amfani da dandalin jama'a domin canza kuɗin zuwa daloli misali, kamfanin zai iya daskarar da su idan ya yi zargin cewa na haramun ne.

Zuwa yanzu, mutum 20 sun samu ladan dala miliyan huɗu saboda nasarar da suka yi wajen gano miliyan 40 na kuɗin satar, inda suka dinga sanar da kamfanonin crypto domin su dakatar da tura su.

"Koriya ta Arewa ƙasa ce mai tsauri wajen sirranta ayyukanta, shi ya sa suke da cikakken tsarin yin kutse da halasta kuɗin haram, kuma babu ruwansu da abin da wani zai ce," in ji Dr Dorit Dor na kamfanin tsaro na Check Point.

Ƙarin wata matsalar shi ne, ba kowane kamfanin crypto ne ke da niyyar taimakawa ba.

ByBit na zargin kamfanin eXch mai hada-hadar canji da wasunsa da ƙin taka wa masu laifiin birki.

An zirarar da kusan dala miliyan 90 ta wannan dandalin. Sai dai shugaban kamfanin, Johann Roberts, ya musanta zargin.

Ya aminta cewa ba su dakatar da kuɗaɗen ba ne saboda suna tsaka da rigima da ByBit, sannan kuma ba su da tabbacin cewa kuɗaɗen na haram ne.

Amma ya ce yanzu suna haɗa kai.

Koriya ta Arewa ba ta taɓa yarda cewa ita ce ta mallaki Lazarus ba, amma ana ganin ita kaɗai ce ƙasa a duniya da ke amfani da ƙwarewarta a harin intanet wajen amfana da kuɗaɗen.

Gungun ya sha kai wa bankuna hari, amma ya fi mayar da hankali kan kuɗin intanet na crypto cikin shekara biyar da suka wuce.

Hare-haren baya-bayan nan da aka alaƙanta da Koriya ta Kudu:

  • Kutsen 2019 kan UpBit na dala miliyan 41
  • Satar dala miliyan 275 na crypto daga kamfanin KuCoin (an ƙwato mafi yawan kuɗin)
  • Hari kan Ronin Bridge a 2022 da suka kwashe dala miliyan 600 na kuɗin crypto
  • Sun sace kusan dala miliyan 100 daga asusun Atomic Wallet a 2023

A 2020, Amurka ta saka wasu 'yan Koriya ta Arewa cikin waɗanda ake zargi da zama mambobin Lazarus a jerin mutanen da ta fi nema ruwa a jallo. Amma kama irin waɗannan mutane abu ne mai wuya, sai dai idan sun fita daga ƙasarsu.