Abubuwan da suka kamata da waɗanda ba su kamata ba wajen ɗumama abinci

    • Marubuci, Nazanin Motamedi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ɗumama abinci ka iya janyo wasu illoli kan lafiyar mutum waɗanda ba a san da su ba saboda haka bin waɗannan shawarwari zai taimaka wajen kiyaye lafiyar abinci da rage yiwuwar kamuwa da cututtukan da ke fitowa daga abinci.

Ga yadda za a iya kiyaye kai:

Abubuwan da bai kamata a yi ba

1. Kada a bar abinci a waje na tsawon lokaci

Kada a bar abinci a wajen da ke da ɗumi na tsawon sa'o'i biyu zuwa hudu. Idan kuma shinkafa ne, kada ya wuce awa guda, domin ƙwayoyin cutar bacillus cereus suna yawaita da sauri a ciki.

2. Kada a sake dumama shinkafar da aka siya daga waje.

Da yake an riga an dafa shinkafar da ake saye a wajajen masu sayar da abinci kuma suna ɗumamawa mutum kafin su siyar, saboda haka sake ɗumama irin wannan shinkafar ka iya janyo illa ga lafiya mutum. Mafi alheri an fi so ci ta da wuri bayan an siya.

3. Kada a ajiye abincin da aka dafa a gida a cikin firiji na dogon lokaci

Yana da kyau mutum ya ci abincin da ya girka a cikin sa'o'i 24 zuwa 48 da dafawa idan ba haka ba kuma a saka a cikin firiza wanda shima kada a bari ya daɗe ciki kafin a ci.

4. Kada a narkar da kazar da ta ƙanƙare da ruwan dumi

Narkar da kazar da ta ƙanƙare da ruwan ɗumi na iya sa wani ɓangare na naman ya yi zafi sosai kafin ya narke gaba ɗaya wanda zai iya janyo ƙwayar cuta kamar ta Campylobacter damar yawaita, cuta da ke janyo matsanancin ciwon ciki, da amai.

A maimakon haka, an fi ba da shawarar a narkar da kaza a cikin firiji sannan a dafa ta har sai ta dahu sosai.

Abubuwan da ya kamata a yi

1. A ajiye abinci a cikin firiji kodayaushe kafin a sake dumamawa

Bincike ya nuna cewa ajiye abinci a cikin firiji da ya sanyi ya kai 5°C ko ƙasa da haka na hana haɓakar ƙwayoyin cuta masu haɗari.

2. A tabbatar abinci ya huce kafin a saka a firiji

Saka abinci me zafi cikin firiji zai iya saka firijin yayi zafi sosai wanda hakan zai iya shafar sauran abinci da ke cikin firijin har ƙwayoyin cuta su fara fitowa, Saboda haka ya kamata abinci mai zafi ya huce kafin a saka a cikin firiji.

3. Ya kamata a fahimci haɗuran da ke tattara da adana abinci

Ƙwayoyin cuta na iya yawaita da sauri a tsakanin sanyin firiji 8°C zuwa 63°C, . Sanya firiji a ƙasa da 5°C yana hana yaɗuwar cututtuka. Sanya abinci cikin firiza a -18°C yana dakatar da aikin ƙwayoyin cuta, amma ba ya kashe su gaba ɗaya – suna iya farfaɗowa bayan an narkar da abincin.

4. A narkar da abinci gabaɗaya kafin a ɗumama

Yana da kyau a narkar da abinci tsawon awa 24 kafin a ɗumama. Ya dangata da girman abincin, idan cikaken kaza ne, zai iya ɗaukar dogon lokaci kafin ya narke. Za a kuma iya narkar da wasu abinci a cikin na'urar ɗumama abinci.

5. A tabbatar abinci ya narke gadaɗaya kafin ɗumamawa.

Idan abinci bai gama narkewa ba, za a iya samun kwayoyin cuta masu ila a ciki.

6. Ya kamata a ɗumama abinci kuma a ci a cikin sa'o'i 24

7. A kula sosai idan ana dumama abincin masu raunin garkuwar jiki

Mutane da ke da ƙarancin garkuwar jiki, masu fama da wasu cututtuka da mata masu juna biyu da ƙananan yara da tsofaffi suna cikin haɗarin kamuwa da cututtukan da ke fitowa daga abinci fiye da sauran mutane.

8. A dumama abinci har sai yana fitar da tururi a ko'ina

Idan ana narkar da abinci a microwave, a juya shi a tsakiyar lokacin domin ya dumamu gabaɗaya..