Abubuwa shida kan Sudan ta Kudu da yaƙi ke dab da ɓarkewa

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Yemisi Adegoke
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Tashin hankali a Sudan ta Kudu bayan kama tsohon mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar.
Jam'iyyarsa ta SPLM/IO ta nuna cewa kama shi ya kawo ƙarshen yarjejeniyar da aka amince ta 2018.
Sudan ta Kudu ta samu ƴancin kai ne a 2011 bayan shafe shekaru da dama tana gwagwrmaya ƙarƙashin jagorancin SPLM da yanzu ke ƙarƙashin shugaba Salva Kiir.
Shekaru biyu da samun ƴancin kai, yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar lokacin da shugaba Kiir ya kori Mr Machar yana zarginsa da ƙulla juyin mulki.
Rikicin na shekara biyar tsakanin ƙabilun shugabannin biyu ya janyo hasarar rayukan mutane kusan 400,000 tare da raba mutane miliyan biyu da rabi da gidajensu.
Me ya sa hakan ke faruwa a yanzu?
Rikicin ya ɓarke ne a watan Maris lokacin da sojojin da ke biyayya ga mataimakin shugaban ƙasa Machar suka gwabza faɗa da sojojin gwamnati a jihar Upper Nile. An kai wa jirgin Majalisar Ɗinkin Duniya hari a lokacin da ya tafi kwaso sojoji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama ciki har da babban janar na soja.
Bayan harin, an kama mataimakin shugaban ƙasa da wasu maƙarabbansa da dama, matakin da jam'iyyarsa ta yi gargaɗi a kai cewa "ya kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiya da aka amince."
"Makomar yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu yanzu ta kamu da babban cikas," in ji Oyet Nathaniel Pierino, mataimakin shugaban SPLM/IO
Wace matsala ce tsakanin Machar da Kiir?

Asalin hoton, Reuters
Duk da shugaba Kiir da mataimakinsa Machar sun taka rawa a SPLM da ta yi gwagwarmayar samun ƴanci, amma akwai tankiya tsakaninsu.
Bambancin ƙabila ne ke rura saɓani tsakaninsu - Shugaba Kiir ɗan ƙabilar Dinka ne yayin da kuma Machar ɗan ƙabilar Nuer - kuma duka suna hamayyar shugabanci.
Lokacin da shugaba Kiir ya kori Mr Machar a 2013, matakin ya haddasa yaƙi, Mr Machar ya ayyana shi a matsayin "mai kama karya"
Ɗage lokacin zaɓe ya ƙara haifar da rikici tsakanin mutanen biyu.
An ɗage zaɓe har sau huɗu, wanda ya hana Machar cika burinsa na shugabancin ƙasa.
Wane ne Machar?

Asalin hoton, Reuters
Riek Machar ya kasance mataimakin shugaban ƙasa a Sudan ta Kudu tun 2011. Yana da digiri na uku a Jami'ar Bradford kuma ya shiga SPLM ne lokacin da ake gwagwarmayar samun ƴanci.
Cire shi muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a 2013 kan zargin juyin mulki, wanda ya musanta ya haddasa mummunan yaƙin basasa.
Wane ne Kiir?
Salva Kiir shi ne shugaban Sudan ta Kudu tun samun ƴancin ƙasar a 2011.
Yana cikin waɗanda suka kafa SPLM, ya zama shuabanta a 2005 bayan mutuwar John Garang.
Wata cibiyar bincike ta Amurka Sentry a baya ta zargi shugaba Kiir da mataimakinsa Machar da cin gajiyar rikicin Sudan ta Kudu, zargin da gwamnati ta musanta.
Girman barazanar
Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu Nicholas Haysom, ya yi gargaɗin cewa kasar "na dab da abka wa yaƙin basasa," wanda zai iya zama bala'i a ƙasar da ke ƙoƙarin farfaɗowa daga yaƙin basasa.
Ana fargabar sake ɓarkewar yaƙin "zai iya haifar da mayaƙa a yankin."
"Akwai mayaƙa masu adawa, da ba su da alaƙa da manyan ƴan'adawa ko kuma shugaban ƙasa, wannan zai iya haifar da ayyukan mayaƙa kan shugaba," in ji Daniel Akech, wani masanin tsaro.
Wane zaɓi ya rage a yanzu?
Tarayyar Afrika ta bayyana cewa za ta tura wakilai zuwa Juba domin ƙoƙarin yayyafa ruwa a rikicin da kuma ƙarfafa tattaunawa.
Kasashe da dama da suka hada da Birtaniya da Amurka da Jamu, sun yi kira ga shugaba Kiir ya janye matakinsa na kamawa da kuma kiran tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.











