Yadda aka tafka asarar kaji sakamakon annobar murar tsuntsaye a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar masu kiwon kaji a Najeriya ta bayyana girman asarar da aka tafka sakamakon annobar murar tsuntsaye.
Ƙungiyar maso kiwon kajin ta ce gonaki da dama ne annobar ta shafa.
Shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano Dr Usman Gwarzo, ya ce shaida wa BBC cewa sai da ya yi asarar gabaki daya kajin da ke wata gonarsa bayan bullar cutar a gonar.
Ya ce tun a 2006 aka fara samun annobar murar tsuntsaye a Najeriya, kuma da farko gwamnati ta yi kamar za ta rika biyan diyya ga wadanda suka yi asarar kajinsu amma kuma abin ya ci tura.
Ya ce," Annobar murar tsuntsayen da ta bulla a baya bayannan ita ce wadda ta zo a lokacin da ake cikin wani yanayi a Najeriya saboda yadda al'amuran tattalin arziki suka tabarbare ga rashin cinikin kaji saboda ba kudi a hannun mutane, sai kuma kwatsam ga cuta ta bulla."
" Jihar Kano na daga cikin jihohin da wannan annoba ta afkawa a watan Nuwambar 2024, kuma an samu babbar asara domin duk inda zai kasance akwai manyan gonaki kamar biyar ko shida na kiwon kaji, to za a ga fiye da rabin gonakin wannan annoba ta bulla." In ji shi.
Dr Usman Gwarzo, ya ce shi a gonarsa, daki daya na kajin ne cutar ta bulla to amma ala tilas dole aka kashe sauran kajin saboda cutar.
Ya ce," A inda gonata ta ke a karamar hukumar Tofa a jihar Kano akwai manyan gonaki shida har da tawa da gaba dayan kajin da ke gonakin suka mutu saboda annobar murar tsuntsayen da ta bulla."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kanon ya ce," Ita wannan annoba na dauke da kwayar cuta ne wadda ba a yi mata magani sai dai rigakafi, to mu a nan Najeriya ba ma yin rigakafinta kamar wasu kasashe, a don haka tun da ba a yi rigakafi ba kuma ciwo ne wanda ke iya yaduwa ga 'yan adam a matsayin mura, don haka da zarar an lura an ga kajin sun kamu da cutar to maganin abin shi ne a kashe baki daya kada cutar ta yadu."
Dr Usman Gwarzo, ya ce," Mun sha kai kokenmu ga gwamnati domin duk wanda annobar ta shiga gonarka ta kaji to ya kan kai rahoto ma'aikatar noma daga nan sai a turo jami'ai daga ma'aikatar su zo su duba hasali ma da su ake kashe kajin to amma babu wani abu da gwamnati ke yi mana hatta wasikar jaje ma bamu taba gani ba."
Ya ce," Mu babban abin da muke so shi ne ya kamata gwamnati da yan siyasa su kula cewa sana'oin da suke dauka da muhimmanci ba sune ke rike tattalin arzikin kasa ba, don a rinka duba wa domin masu kiwon kaji ma na da muhimmanci musamman wajen ciyar da tattalin arziki gaba.
Ya ce, " Kowa na cin kaji musamman su manyan kasa to amma idan masifa ta afkawa masu kiwon kajin a yi biris da mu."
"A don haka a duba a yi mana maganin wannan annoba ta murar tsuntsaye ta hanyar samar da rigakafinta a kasa." In ji shi.











