An nemi ɗauki bayan ƙudajen zuma miliyan biyar sun faɗo daga mota

Asalin hoton, Getty Images
Wani mai kiwon zuma, Michael Barber ya farka da safiyar ranar Laraba, 'yan sanda na ta kiran wayarsa saboda suna neman taimako bayan ƙudan zuma miliyan biyar sun faɗo daga wata babbar mota a Kanada.
An ɗauko amiyoyin zuma ne don tafiya da su amma sai igiyar da aka ɗaure su ta ƙunce, lamarin da ya sanya ƙudajen zuma tashi, inda suka fantsama cikin gari.
Mista Michael Barber ya ce ya isa wurin da ya samu "wani hadarin ƙudajen zuman da suka birkice" waɗanda kuma "sun yi matuƙar fusata, kuma suna cikin ruɗani da rashin gida".
An faɗa wa masu motoci su ɗaga gilasan abin hawansu, masu tafiyar ƙafa kuma aka umarci su kauce daga yankin.
Mai yiwuwa ne Michael Barber bai taɓa ganin wuri irin na boren ƙudan zumar da ya faru a Burlington cikin birnin Ontario ba a tsawon shekara 11 na sana'arsa.
"Lamarin ya zama wani iri daban," ya faɗa wa BBC. "Ina fata hakan ba zai sake faruwa ba."
Mista Barber, wanda ya mallaki Kamfanin kai Ɗauki ga Harin Ƙudan Zuma na Tri-City a kusa da yankin Guelph, ya ce da farko 'yan sanda sun kira shi ne misalin ƙarfe 7, inda suke sanar da shi cewa an samu wani hatsari da ya janyo amiyoyin ƙudan zuma suka faɗo a kan titi.
A lokaci guda kuma, 'yan sanda sun buga sanarwa a shafukan sada zumunta inda suke neman mutane su janye jiki daga yankin, wanda ya kasance a wani wuri mai nisan tafiyar sa'a ɗaya a kudancin Toronto.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙudajen zuman suna cikin amiyarsu cushe a bayan wata babbar mota, inda ake tafiya da su zuwa mashekarinsu na lokacin hunturu sa'ar da hatsari ya faru.
'Yan sanda na kiran Michael Barber, shi kuma ya riƙa kiran sauran takwarorinsa masu kiwon zuma don su kawo ƙarin ɗauki.
Gomman masu kiwon zuma ne daga bisani suka taimaka wajen tattara ƙwarin.
Mai kiwon ƙudan zuman ya ce zumar da amiyoyinsu sun wawwatsu a wani wuri mai faɗin sama da mita 400. Matasan ƙudan zuma sun yi cincirindo a kan motoci da cibiyoyin aika saƙonnin gidan waya da ke kusa, a cewarsa haka ƙwarin ke yi a duk lokacin da suke neman wuri mai aminci.
"Ƙudan zuma mai yiwuwa kimanin dubu ɗaya ne suka hau gaban motata," in ji shi.
Sauran zuman, waɗanda ga alama sun fi fusata da tsufa, na ta zarya da guna-guni a zagayen.
Bayan sa'o'i ƙalilan, mafi yawan ƙudan zuman sun iya samun amiyoyinsu, a cewar Mista Barber, amma akwai wasu 'yan ɗaruruwa da ba su iya kuɓuta daga hatsarin ba.
Zuman dai sun harbi wasu masu kiwonsu da ke ƙoƙarin tattara su wuri ɗaya.
Kuma sun harbi direban motar da ta ɗauko fiye da sau 100, a cewar Mista Barber, kafin ya kai ga sanya cikakkun rigunan kariya. Akwai ma'aikatan lafiya a kusa, don haka bai ji matsanancin rauni ba.
"Akwai dandazon ƙudan zuma da ke zarya a sama waɗanda suka sanya hatta masu kiwon da suka zo tattara su, cikin fargaba," in ji shi.











