Yadda raguna suka yi kwantai a Nijar

Raguna
Lokacin karatu: Minti 2

Masu sana'ar sayar da dabbobi a Nijar na ci gaba da kokawa da yanayin da suka tsinci kansu, bayan matsalolin da matakin gwamnatin ƙasar na hana fita da dabbobi ƙasashen waje ya haifar.

A kasuwannin dabbobin da ke birnin Yamai, raguna na nan maƙare babu ma su saya lamarin da ma su sayar da ragunan suka ce ya janyo mu su asara mai dumbin yawa.

Wasu ma su sayar da ragunan da BBC ta tattauna da su a Yamai, sun ce wasu ragunan har mutuwa suke yi, ga asarar da suke yi saboda ba a saya.

Malam Inusa mai kawo dabbobi ne kasuwar Yamai daga Tasawa ya shaida wa BBC cewa a yanzu dabbobi na nan birjik babu ma su saya.

Ya ce, "Ga ragunan nan har babu ma inda za a ajiye su saboda yawansu amma babu masu siya tun da yanzu a wuni guda da ƙyar za ka sayar da rago guda, idan ka yi sa'a ne ma a wuni guda za ka sayar da biyu, don haka ala dole mu ka saukar da farashin ragunan."

Alhaji Lawwali Kalla, mazaunin Yamai ne ya shida wa BBC cewa ba wani abu ba ne ya janyo rashin siya raguna illa albashin ma'aikata da ba a biya ba.

Ya ce, "Da yawan ma'aikata sun ce ba a biya su albashi ba, shi ya sa ma ba su je sun sayi ragunan layyar ba, kuma su masu sayar da ragunan ba bashi suke bayarwa ba sannan kuma ga lokaci na kurewa.."

Kwantan raguna a Jamhuriyar ta Nijar din na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar sallar layya ta shekarar 2025 wato ga ma su iko.

A watannin baya ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da haramcin fitar da dabbobi daga ƙasar zawu ƙasashen waje ciki har da Najeriya.

Alƙaluman cinikayyar ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun nuna cewa a shekarar 2023 kawai Nijar ta fitar da dabbobin da suka kai na dala miliyan 3.93 zuwa Najeriya.

Ministan kasuwancin ƙasar ya ce gwamnati ta umarci jami'an tsaro su ɗau matakan da suka dace a kai da kuma hukunta duk wanda ya saɓa wa sabuwar dokar.