Firgicin da waɗanda suka tsira daga girgizar ƙasa ke fuskanta

Adadin mutanen da suka mutu a mumunar girgizar kasar da ta afkaqa kasashen Turkiyya da Syria a kwanan nan ya zarce 44,000, sannan ta raba dubban da muhallansu.
Lamarin ya shafi lafiyar kwakwalwar wasu da dama da ibtila’in ya shafa. BBC ta tattauna da wadanda suka tsira, da tawagar masu aikin ceto, da kuma kwararru.
Motarmu ta lalace kuma direban da aka sauya mana ya gaza daukar mu zuwa tsakiyar birni.
Kwanaki uku bayan girgizar kasar ta afka wa yankin kudu maso gabashin Turkiyya.
Tawagarmu tazo ne daga Maras, yankin da girgizar kasar tafi kamari.
Tuni an riga an tabbatar da mutuwar dubban mutane kuma adadin ya cigaba da karuwa tun daga lokacin faruwar lamarin.
A yayin da muka isa babban titin zuwa Antakya, ana ta samun karar jiniyar motocin daukar marasa lafiya babu kakkautawa a burabuzan gine-gine.
Motocin aikin ceto, da motocin bulldozers da masu ayyukan sa-kai dukkansu sun yi jerin gwano.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanayi ne mai cike da dimuwa sakamakon yanayin tsananin sanyi.
Burak Galip Akkurt da tawagarsa na kungiyar ma’aikatan sa-kai masu aikin ceto na Turkiyya, Akut, yana aiki a wani bene mai hawa hudu.
Suna tsammanin akwai mutane 10 dake karkashin burabuzan gini, biyar daga cikinsu kananan yara ne.
Fitilun da suke aiki dasu a duhu a burabuzan gine-gine a yayin da suke cigaba da yin wata tambaya da ta zama ruwan dare a kasar Turkiyya, tambayar it ace; “Akwai wanda ke ji na?"
Suna sauraro cikin natsuwa, suna fatan ko zasu ji sautin wata muryar da zata amsa musu koda kuwa wani motsi ne, ko kada yatsa, ko kuma dannawa.
"A yayin da aka ji wata murya dake fita daga karkashin ginin da ya rufta, yaya kake ji?" Na tambayi Burak.
Yana kokarin danne damuwar da yake ji don ya samu damar gudanar da ayyukansa na ceto, ya bayyana cewa, lamarin na damunsa da zarar ya kammala aikin, kuma yana bukatar taimakon kwantar masa da hankali don jure yanayin da ya fuskanta.
"Abu ne mai matukar wahala ka dawo cikin hayyacinka game da abubuwan da ka gani. Akwai firgici, kuma akwai matukar tashin hankali."
Babu koda mutum guda da aka ceto da rai a burabuzan ginin benin da ya rufta inda suka gudanar da aiki a wannan dare.
Washe gari na gamu da Dilek Eger. Wacce aka cetota daga wani gini a garin Iskenderun mai makwabtaka, bayan da ginin ya binneta har tsawon sa’oi takwas.
"Girgizar tana da matukar karfi. Na tashi a figice daga kan gado kuma na nufi dakin iyayena. Ina kwarma ihu huhuna sun fito waje. Amma mahaifiyata, da mahaifina, da danuwana, duka sun yi shiru. Na zaci zan hankali nay a gushe ne," kamar yadda ta fada mini.
Iyayen Dilek da danuwanta sun rasa rayuwarsu a ginin da ya rufta. Ta makale, inda wasu fasassun gilasai suka danneta, kanta kadai ake iya gani. Yan uwa da abokan arziki sun ganeta tare da cetota ta hanyar amfani da hannaye dakuma wuka.
An gaza ceto a kwanaki biyun farko, amma kasancewar tana kwance ne kan soson katifa a falon kakarta, tana Magana dani a hankali cikin yanayin rashin jin dadi, sannu a hankali ta fara warwarewa daga halin da take ciki.
A yayin da ta sumbaci hoton mahaifiyarta da rumgume hoton, sai ta fara kuka.
"Numfashin karshe na mahaifiyata ya fita tana hannuna,"a cewarta. "Har lokacin da take mutuwa, ta ceto ni, a lokacin da take samana. Babu abinda zan iya yi mata.
"Dan uwana ya makale a wani daki, babana kuma yana fama da tsananin ciwo. Wannan shine lokacin da duniya ta zo karshe. Kuna fuskantar mutuwar dukkan masoya.
Dilek na daya daga cikin dubban mutanen da suka tsira a girgizar kasar, amma a yanzu yana fuskantar wata irin rayuwa mafi muni.
A wannan makon na samu rubutaccen sako daga wani mutumin da tsira. Ya rubuta cewa, "Wasu daga cikinmu dake rayuwa a doron duniya zasu cigaba da kasancewa karkashin burabuzai har zuwa ranar da zamu mutu."
Masana halayyar dan adam sun ce wadanda suka tsira a wannan mummunan iftila’in zasu fuskanci wasu matakai na fargaba, damuwa, da kuma tsoro.
Cagay Duru daga kungiyar masana halayyar dan adam ta Turkiyya, sun ce ba abu ne mai sauki a iya jure irin wannan yanayin firgici mai girma ba, amma Magana game da batun, da bayyana damuwa da tunani game da abinda aka fuskanta zai zmaa matakin farko na samun waraka.
Yayi gargadin cewa, idan ba a samar da taimakon sauya tunani da lallashi ga mutanen da suka fuskanci tashin hankalin ba, mutane da dama zasu iya fadawa cikin yanani mai muni, kamar cutar damuwar bayan fuskantar bala’i, da kuma kuncin rayuwa.
"Dukkanmu ya kamata mu dinga tambayar junanmu cewa: Yaya kake? Ko akwai wani abinda zan yi maka?
"Sai muce: Nazo nan ne saboda kai. Dole mu gabatar da sakonnin nuna goyon baya ga masu bukatar taimako kuma dole mu yi kokarin fahimtar abubuwan da suka fuskanta, muna nan domin sauraronsu, mu taimakesu kuma mu tattauna dukkan wadannan damuwa da aka fuskanta."
Daidaituwar al’amurra bay ana nufin komawa rayuwa irin ta kafin faruwar girgizar kasa ba, yana nufin komawa sabuwar rayuwa. Akwai bukatar gina sabuwar raywar kuma zai dauki dogon lokaci.
Amma wannan aiki ya gamu da koma baya ne bayan da aka samu afkuwar sabuwar girgizar kasa da ta faru bayan ta farko a garin Hatay.
A yanzu Istanbul, na bar yankin da iftila’in ya faru, amma har yanzu ina kewaye da yanayi mai firgici. A yayin da tashin hankalin ya faru, firgici mai yawa da yadda za a tinkaresu sune manyan kalubalolin ga kasar Turkiyya.











