Mutumin da ya shekara 56 yana hawan keken da ya siya naira shida
Malam Garba Nayamma ya kwashe shekaru 56 yana tuka keken da ya saya a zamanin tsohohn shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon.
"Na sayi wannan keken ne fam uku wato naira shida kenan kuma har yanzu sai dai kawai idan wani abu ya lalace na sauya."
Malam Garba ya ce a tsawon shekarun nan da ya kwashe yana amfani da keken, da shi yake zuwa gona da ma duk wata ziyara da yake yi a garuruwan arewacin Najeriya.
"Duk yawon 'yan matanci da muka yi da wannan keken muka yi shi. Na kan dauki abokaina domin zuwa zance inda nake dora daya a gaba sannan daya kuma a kan kariya."
Ya kara da cewa a duk lokacin da aka dauke min wannan keken to lallai an takaice ni kasancewar shi ne abun hawana da na riga na sani.
Duk da cewa malam Garba ya tsufa domin ya wuce shekara 70 da haihuwa amma da kwarinsa watakila saboda irin shekarun da ya kwashe yana tuka wannan keke wanda hakan motsa jiki.
"Ba ni da wata cutar da ke damu na."









