Yadda Donald Trump ya titsiye shugaban Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Gary O'Donoghue
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Chief North America Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Wata uku kenan da Donald Trump ya soma wa'adinsa na biyu, shugabannin ƙasashen waje su yi hattara tare da sani cewa duk wata ziyara a ofishin shugaban ƙasa na Oval Office, na iya zama haɗarin titsiyewa da zubar da kima, inda galibi kullum akwai niyyar tayar da hatsaniya da cin fuska.
Lamarin da ya faru a ranar Laraba tsakaninsa da shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na daban ne, da aka samu yanayi mai kama da kwanton ɓauna da rage hasken da aka yi akai-akai da nuna dogayen bidiyo tare da kawo wasu sassan labarai da aka riga aka shirya.
Bayan da aka kammala tattaunawa mai zafi tsakaninsu sai manema labarai suka tambayi Trump ko ta ya zai gamsu cewa iƙirarin an yi "kisan ƙare dangin ga fararen fatar" Afirka ta Kudu ba gaskiya ba ne.
Da farko Ramaphosa ya mayar da martani inda ya ke cewa a ya dace Trump ya "saurari damuway 'yan Afirka ta Kudu" akan batun. Nan take Trump ya katse shi inda ya umurci hadiminsa "ya rage hasken zauren" ya kuma kunna talabijin domin ya nuna ma shugaban Afrika ta Kudun "abubuwa biyu".
Duk abin da ake yi a lokacin Elon Musk wanda mashawarcin Trump ne, kuma hamshaƙin biloniya ne ɗan Afirka ta Kudu yana can a baya tsaye yana kallo.
Abin da ya faru ba a saba ganin irin sa ba, saboda abu ne a shugaban Amurka ya tsara da gangan domin ya jefa zargi game da kisan fararen fatar Afirka ta Kudu, ya zama tamkar maimaita abin da ya faru ne ga shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a lokacin zaiyar da ya kai Fadar White House a watan Febrairu.
Hotunan bidiyon sun nuna wasu 'yan siyasar Afirka ta Kudu na rera cewa "a harbi Boer (manomi), wadda waƙa ce mai nuna ƙin jinin mulkin wariya. Ga alama Trump wanda mutum ne da mafi yawan lokuta ya ke sukar kafafen watsa labarai, ya nuna jin daɗin nuna hotunan da babu tabbacin sahihancinsu. Da aka tambaye shi ina ƙaburburan fararen ftar da ya ke zargin an kashe, kawai sai ya bada amsar cewa, "a Afirka ta Kudu".
Shugaban na Amurka ga alama dai ya gamsu da cewa shugabannin siyasar da aka gani a bidiyon - waɗanda ba su cikin gwamnatin ƙasar - suna da ikon ƙwace gonakin fararen fata. Alhali ba su da ikon yin haka.
Yayin da a hannu ɗaya Ramaphosa bai saka hannu akan ƙudurin dokar da ya bada damar ƙwace filaye ba tare da biyan diyya ba, kan haka ba a ƙaddamar da dokar ba. Kuma ya nesanta kansa a gaban jama'a daga kalaman da aka yi a jawaban da aka nuna.

Asalin hoton, Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tattaunawarsu game da makomar manoma fararen fata ta ɗauki tsawon lokaci ne akan akwatin talabijin da aka kunna a ofishin na Trump, sai dai shugaban Afirka ta Kudun, duk da ya natsu a lokacin, amma ya rinƙa kare kansa.
Amma Ramaphosa ya yi farin ciki cewa a tare da shi akwai ministansa na noma, wanda ya fito daga jam'iyyar hammaya bayan da aka kafa gwamnatin haɗin gwiwa, yana tare da shi a matsayin garkuwa, wani tsari na diflomasiyya wanda kuma ya yi amfani.
Nan take Trump ya juya akan makomar manoman - waɗanda ya riga ya tarbi gomman su a Amurka a matsayin 'yan gudun hijira. Amma shugaba Ramaphosa bai yi magana ba kasancewar cin fuskar ya wuce misali.
Kan haka ma ya ya nuna fitattun 'yan wasan ƙwallon golf tare da su fitaccen mai kuɗin ƙasar da ya je tare da su a tawagarsa, ya shaida wa Trump cewa,."Da akwai wani abu wai kisan ƙare dangi, ina mai tabbatar maka da waɗannan jama'a ba su kasance a nan ba".
Wannan irin salon tsarin diflomasiyya a da manufar tayar da tsimin magoya bayan Trump, tare da kirarin nan nasa na 'Sake Ɗaukaka Amurka' (MAGA), da ke nuna jiji da kai irin na Trump wanda ya riga ya san abin da magoya bayan nasa suke muradi kenan.
Idan har hakan zai zama darasi ga shugabannin ƙasashen waje su koyi yadda za su san makamar tafiyar da irin waɗannan lokuta tare da nuna ƙwarewa, to dole Donald Trump ya canza irin salon da ya ke amfani da shi na yi wa kowa yadda ya ga dama.












