Qatar 2022: Croatia ta tsallaka semi fayinal bayan doke Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar ƙwallon ƙafar Croatia ta doke ta Brazil a bugun finareti a wasan zagayen kwata fayinal da suka fafata na Gasar Kofi Duniya da ke gudana a Qatar.
Croatia ta yi nasara da 4-2 bayan wasa ya tashi 1-1.
Rodrygo da Marquinhos ne suka zubar da finaretin, inda mai tsaron raga Livakovic ya doke ɗaya, ɗayar kuma ta bigi turke.
An buga wasa tsawon minti 105 kafin Neymar ya ci wa Brazil ƙwallon farko. Saura minti huɗu a kammala zagaye na biyu na ƙarin loƙaci ne kuma Petkovic ya farke ta.
Jimilla, Neymar ya ci wa ƙasarsa ƙwallo 77, abin da ya sa ya kamo tauraron ɗan wasa Pele a yawan adadin da suka ci wa tawagar ƙasarsu.






