Ba matakan Tinubu ne ke kawo sauƙin abinci a Najeriya ba — ADC

Asalin hoton, X/ADC
Jam'iyyar hammaya ta ADC a Najeriya ta ce babu ƙamshin gaskiya a ikirarin da gwamantin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi cewa matakan da take dauka ne ke kawo saukin farashin kayan abinci a kasar.
ADC, ta bayyana damuwa kan abin da ta kira da labarin yaudara daga gwamnati kan cewa ta kawo saukar farashin abinci ga al'umma.
Kazalika jam'iyyar ta ce duk wani sauki da ake gani a kasuwa, ya faru ne sakamakon tsoro da rudani da kuma rashin daidaiton kasuwa, baya ga matsalar tsaro da ta addabi manoma musamman a yankunan arewacin ƙasar inda manoma ke gaza samun nasara a fannin noma.
Faisal Kabiru, ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya shaida wa BBC cewa idan aka yi la'akari za a ga cewa manoma a Najeriya na amfani da abubuwa kamar man fetur da wajen noman kamar su tattasai da tumatur da albasa da sauransu, kuma da tsada suke sayensa, to amma lokaci guda gwamnati ta zo ta karya wannan kaya na masarufi.
Ya ce," Kayan da ake shigowa da su daga wajen wadanda ake amfani da su, a kullum kara tsada suke maimakon su sauka, to amma me ya sa aka karya farashin wanda ake nomawa a gida bayan manoman na kashe makudan kudade wajen yin noman?."
"Idan ka tambayi manoman Najeriya a cikin kashi 100, to ko shakka babu kashi 90 cikin 100 din nan za su fada maka cewa idan shekara ta zagayo ba za su iya yin noma ba saboda ba su da jari, sakamakon karya musu farashin kayan da suka noma da gwamnati ta yi."In ji shi.
To sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan wannan zargi, inda ta ce adawa ce kawai ADC ke yi da nasarorin nata, wanda ta yi iƙirarin cewa a bayyane suke.
Abdulaziz Abdulaziz, daya daga cikin masu magana da yawun shugaba Tinubu ya shaida wa BBC cewa, masu adawar su suka rika ihu suna cewa kayan abinci sun yi tsada, to yanzu gwamnati ta dauki matakan kawo sauki, kuma sai ga su suna kokawa.
Ya ce," 'Masu wannan zargi 'yan adawa ne ba zasu taba ganin alheri ba, don haka su fadi irin wadannan maganganun ba abin mamaki ba ne.
"Masu cewa sun rasa jarinsu saboda saukar farashin kayan abinci, to ba mamaki irin mutanen nan ne da suka dauki noma hanyar tsawwalawa mutane, domin wadanda ke nom ana tsakani da Allah ai ba za su ce haka ba."In ji shi.
A watan Satumbar da 2025 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni ga wani kwamitin gwamnatin tarayya ya aiwatar da matakan gaggawa, domin sake karya farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.
Wannan mataki ya zo ne a dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubale na tsadar rayuwa.
Duk da cewa an fara ganin sauƙi a farashin wasu kayan abinci a kasuwanni daban-daban na Najeriya, wasu daga cikin manoman ƙasar na zargin matakin ya karya su tare da haifar musu da ɗumbin asara sakamakon tsadar kayayyakin da suke amfani da su wajen yin noman.











