Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iwobi ya tsawaita zamansa a Everton
Dan wasan tsakiyar Najeriya Alex Iwobi, ya aminta da sabuwar yarjejeniyar tsawaita zamansa a Everton da ke buga gasar Premier a Ingila.
Iwobi mai shekaru 26 zai cigaba da zama kungiyar ta Goodison Park har zuwa 2024.
Dama an dade ana tattauna batun tsawaita zaman na Iwobi a Everton, kuma a yanzu an kai karshe.
A sabuwar yarjejeniyar Iwobi zai rika karbar albashin fam dubu 90 a duk mako.
Tsohon dan wasan na Arsenal ya buga duka wasanni 15 da Everton ta buga kafin aje hutun gasar Qatar 2022, kuma ya taimaka anci kwallo shida, inda ya ci daya a wasan da kungiyar ta yi da Manchester United.
A 2019 ne Alex Iwobi ya tafi Everton, kuma kawo yanzu ya buga mata wasanni 114.
A Arsenal kuwa ya buga wasanni 149, bayan an yaye shi daga tawagar matasan Gunners.
A wata mai kama da haka Everton ta dab da cimma sabuwar yarjejeniya da matashin dan wasan Ingila, Anthony Gordon, wanda Chelsea ta nace tana so ta dauka.