Wace ibada aka fi so a ranar Juma'a?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ranar Juma'a ta kasance wata babbar rana mai gwaɓi ga al'ummar Musulmi a duniya, wadda malamai da dama ke ayyana ta da tamkar Idi.

Malamai na yawan kwaɗaitar da jama'a su zage dantse wajen yawaita ibada da addu'o'i a darenta da ranarta.

To sai dai abin da ke shigar wa jama'a da dama duhu shi ne wace irin Ibadar ce ta fi kowacce a wannan rana domin samun babban lada.

Ibadar da aka fi so ranar Juma'a

..

Asalin hoton, Daurawa/Facebook

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hizba a Kano kuma malamin addinin, a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce ibadar da ta fi kowacce a wannan rana ita ce salatin annabi.

"A ranar Juma'a ya zama mafi yawan ibadar da za ka yi ita ce Salati ga manzon Allah. Haka ma a daren Juma'a ka ajiye duk wani abu kamar karatun Ƙur'ani da tasbihi da tahmidi da tahlili ka yi ta salatin annabi. Haka ma kuma a ranar Juma'a," in ji Sheikh Daurawa.

Duk da dai Sheikh Daurawa bai faɗi adadin yawan salatin da ya kamata mutum ya yi ba amma ya nanata buƙatar yawaitar salatin a wannan rana mai albarka.

Mece ce ribar salati?

Sheikh Daurawa ya ƙara da cewa babbar ribar yawaita salati ita ce samun ninkin abin da mutum ya ambata daga ubangiji da kansa.

"Duk wanda ya yi min salati guda ɗaya to Allah ubangiji zai yi masa salati ƙafa 10. Ba mala'ika ba Allah ne da kansa zai yi wa wanda ya yi wa annabi salati ƙafa ɗaya shi kuma Allah ya yi masa ƙafa 10," in ji Sheikh Daurawa.

Fitaccen malamin ya ƙara da cewa "Annabi Muhammad SAW ya ce mutumin da ya fi kusanci da ni a aljanna shi ne wanda yake yawaita yi min salati."

Sheikh Daurawa ya jaddada cewa " saboda haka ya kamata Musulmi su guji gulma da musu da hayaniya a wannan rana su mayar da hankalinsu ga salatin annabi wanda shi kaɗai zai sauya rayuwarsu."

Mene ne tasirin Allah ya yi maka salati?

Sheikh Daurawa ya ce bai kamata mutane su yi sakaci da wannan garaɓasa ba wadda Allah da kansa zai yi wa ɗan adam salati da hakan zai sauya rayuwar mutum.

Malamin ya kawo misalai dangane da yadda mutum ke neman addu'ar bayain Allah da yadda hakan ke tasiri a rayuwarsa ballantana kuma Allah ubangiji da kansa.

Babban tasirin hakan dai bai wuce samun albarka ga kai da zuriya da biyan buƙata da kuma shiriya.