Chelsea ta ɗauki Essugo daga Sporting mai wasan aro a Las Palmas

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta amince da biyan £18.5m ga Sporting, domin ɗaukar Dario Essugo, wanda ke wasannin aro a Las Palmas.

Mai shekara 20 an yi masa tayin yarjejenuyar kaka bakwai da rabi da cewar za a tsawaita masa shekara ɗaya idan ya yi abin kirki.

Kenan ɗan wasan tawagar Portugal zai koma Stamford Bridge a watan Yuni, zai ke aikin mataimakin Moises Caicedo da zarar ya ci karo da cikas.

Wata majiya daga Stamford Bridge ta ce matashin ya burge masu ɗaukar ƴan wasa a ƙungiyar, bayan da aka bibiyi wasanninsa a kakar nan.

Chelsea na sa ran yin amfani da Essugo a watan Yuni, domin ya fara taka leda a Club World Cup da za a yi a Amurka.

Essugo ya buga wa Sporting wasa 25 a bana daga nan ta bayar da aronsa Las Palmars ta Sifaniya, wadda ya yi wa karawa 17

Haka kuma Chelsea ta kammala sayen matashi mai shekara 17, Geovany Quenda daga Sporting kan £40m a makon nan.