Me ya sa ba ma iya tuna lokacin da muke jarirai?

Asalin hoton, KDP via Getty Images
- Marubuci, Maria Zaccaro
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Ranar da aka haife mu, ranar da muka fara tafiya, kalmar farko da muka fara furtawa duk wasu muhimman abubuwa ne a rayuwarmu. Amma ma ba iya tuna kowanensu. Ko me ya sa?
Masana kimiyyar ƙwaƙwalwa da masana halayyar ɗan'adam ke fama da ita cikin gomman shekaru.
Kasa iya tuna muhimman abubuwan da suka faru da mutum a lokacin da yake jariri shi likitoci ke kira ''lalurar kasa tuna lokacin kaka jariri'', kuma masana kimiyya sun shafe shekaru suna samar da bayanan kansa.
Farfesa Turk-Brwone masanin halayyar ɗan'adam kuma likitan ƙwaƙwalwa a Jami'ar Yale da ke Amurka ya ce an jima ana muhawara kan tambayoyi biyu:
- Muna iya riƙe abubuwa a lokacin da muke jarirai, amma mu kasa tuna su idan un girma
- Ko ba ma iya fara riƙe abubuwa a ƙwaƙwalwarmu har sai mun girma?
Farfesa Turk-Browne, ya ce a baya masu bincike sun ɗauka cewa jarirai ba sa iya tuna abubuwa.
Wasu cikin masanan sun yi imanin cewa hakan na faruwa ne saboda rashin kammala halittar ƙwaƙwalwarsu ko rashin iya magana.

Asalin hoton, Science Photo Library via Getty Images
Masanin ya ƙara da cewa na ma iya riƙe abubuwa a ƙwaƙwalenmu har sai mun kai shekara huɗu, saboda a lokacin ne aka kammala halittar ''hippocampal'', wani ɓangaren ƙwaƙwalwa da ke iya riƙe abubuwa da tunasu.
"Ba a kammala halittar wannan sashe har sai mutum ya kai shekara huɗu," a cewar Farfesa Turk-Browne.
"Don haka a lokacin ba za mu iya riƙe wanu abu a cikin ƙwaƙwalwarmu ba, ballanatana ma mu tuna shi daga baya," in ji shi.
Ɗaukar hoton ƙwaƙwalwar jarirai
To sai dai wani sabon bincike da aka wallafa a farkon wannan shekara wanda shi kansa Farfesa Prof Turk-Browne ya gudanar ya saɓa wa wannan tunani.
Tawagar binciken ta nuna wa wasu jarirai - masu shekaru tsakanin wata huɗu zuwa shekara biyu - wasu jerin hotuna domin gwada ƙwaƙwalwarsu da auna aikin ''hippocampal''na ƙwaƙwalwar tasu.
Sannan daga baya suka nuna wa jariran ɗaya daga cikin hotunan tare da wani sabo domin lura da yadda idanunsu suka riƙa motsi wajen tantance hotunan biyu domin fahimtar wanda suka fi kalla.
Yayin da suka kuma binciken ke amfani da na'urar zamani wajen ɗaukar hoton ƙwaƙwalrwar jariran a lokacin da suke kallon hotunan
Idan tsohon hoton suka fi kalla, amsu bincike za su ɗauki hakan a matsayin hujjar cewa jarirai sun iya tuna hoton sun kuma gane shi, saɓanin yadda nuna a binciken farko ba.

Asalin hoton, 160/90
Masu binciken sun gano cewa ''hippocampus'' na ƙwaƙwalwar jariran na aiki yadda ya kamata a lokacin da suke kallon hoton a akaron farko, don haka akwai yiyuwar za su iya tuna shi daga baya - musamman idan sun haura wata 12.
Wannan na nuna cewa kwakwalwar yara na iya riƙe abu idan yaro ya kai shekara guda.
Me ya sa ƙwakwalwa ba ta iya tuna abin da ya faru a lokacin jariri?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Turk-Browne ya ce binciken tawagarsa ''matakin farko ne'' na gano cewa idan jarirai na iya taskance abu a cikin ''hippocampus'' ɗinsu.
Don haka har yanzu akwai buƙatar faɗaɗa bincike.
"Idan muna iya riƙe abubuwa a lokacin da muke jarirai, to hakan zai haifar da sabuwar tambayar cewa me ya sa ba ma iya tuna su idan mun girma?
''Shin har yanzu suna nan?, za mu iya tuna su?'', kamar yadda ya yi bayani.
Wani bincike da aka wallafa a shekarar 2023 ya gano cewa ɓerayen da suka koyi hanyar fita daga ƙwararonsu tun suna jarirai sun manta da hakan a lokacin da suka girma.
Amma ta hanyar amfani da fasahar zamani na wucin-gadi a ''hippocampus'' na ƙwaƙwalwar da ta iya riƙe abubuwa a baya, zai taimaka wajen iya tuno da su.
Sai dai har yanzu ba za a iya tabbatar da ko ƙwaƙwalen mutane za ta tuno abubuwan da ta iya riƙe su a lokacin da suke jarirai ba.
Farfesa Catherine Loveday, ƙwararriya a fannin ilimin ƙwaƙwalwa a Jami'ar Westminster da ke Birntaniya, ta yi iamnin cewa jarirai za su iya riƙe abu a ƙwaƙwalwarsu, aƙalla in sun kai lokacin fara magana.
"Mun sani cewa ƙananan yara kan dawo daga makarantar renon yara, su bayyana mana wani abu da ya faru, wanda bayan shekaru ba za su iya tuna shi ba. Don haka suna iya riƙe abu, kawai dai baya jimawa a ƙwaƙwalwar,'' kamar yadda ta yi ƙarin haske.
"Ina ganin akwai tsawon wani lokaci ƙwaƙwalwar jarirai ke iya riƙe abu kafin ta manta shi, da kuma irin lokacin da ƙwaƙwarwar ke ɗauka tana tuna abubuwa masu kamanceceniya da shi'', in ji ta.

Asalin hoton, ullstein bild via Getty Images
''Tuna wani muhimmin abu''
Farfesa Loveday ya ce abin da ta ƙara dagula fahimta game da tunanin jarirai, shi ne tabbatar da ko wani abu da mutane ke tunanin shi ne farkon abin tunawa.
Alal misali wasu daga cikinmu ka iya tuna wani muhimmin al'amari da ya faru da su a lokacin da suke ƙanana.
Farfesa Loveday ta ce irin waɗannan abubuwa ba a iya manta su wataƙila saboda yadda suka faru.
"Wani abu game da tuna abu a ƙwaƙwalwa shi ne koyaushe ana sake iya fasalta shi. Idan wani ya faɗa maka wani abu, kuma ka samu cikakken bayani kan abun, ƙwaƙwalwarka za ta iya hakaito shi a gaske, koda ba ka taɓa ganinsa ba'', kamar yadda ta yi ƙarin haske.











