Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cocin Katolika ta bukaci a dakatar da Lalong kan zargin 'saɓo'
Wata takaddama ta kunno kai a Najeriya tsakanin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong da Mabiya addinin Kirista ‘yan darikar Katolika bayan wasu kalamai da gwamnan ya yi cewa Fafaroma Francis bai ga laifin karbar mukamin darakta-janar na kamfe din dan takarar shugaban kasa a APC Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba duk da cewa dukkansu Musulmai ne.
Wannan dai ya fusata kiristoci mabiya katolika wadanda suka bayyana ambato sunan Fafaroma a zaman raini ga jagoran nasu.
Hakan ya sa suka yi kira a dakatar da shi daga zaman dan darikar.
A wani taron manema labarai da mabiya darikar katolika a Najeriya mai suna Concerned Catholics in Nigeria suka gudanar a Abuja, sun bukaci a dakatar da Simon Lalong daga darikar saboda kiran sunan shugaban darikar na duniya, Fafaroma Francis cikin harkokin siyasa wadda ba ta da alaka da da cocin.
Kalaman ba su dace ba
Kiristoci da dama dai na mayar da martani kan kalaman da Gwamna Simon Lalong din ya furta kan fafaroma Francis.
Rabaren John Joseph Hayep shi ne Shugaban Kungiyar Kiristoci shiyyar arewacin Najeriya, ya ce bai kamata Lalong ya furta kalaman da ya yi ba saboda ba shi ne kirista na farko ba da aka taba bai wa darektan yakin neman zaben wani dan takarar shugaban kasa.
"Daraktan kamfen na Shugaba Buhari Rotimi Amaechi ne wanda kuma dan Katolika ne, ya yi aiki. A matsayinka na shugaba, idan an ba ka aiki idan akwai wata damuwa kokarin kwantar da ita za ka yi'’.
Rabaren John Hayep ya kara da cewa kalaman da Gwamna Simon Lalong ya yi na kokarin zargin addini ne da kuma makantar da idonsa ga gaskiya da kuma furta abin da bai dace ba saboda siyasa da son zuciya.
''Mu a ganinmu wannan bai dace ba,’' in ji Rabaren John Hayep.
Martanin Gwamnatin Filato
A wata sanarwa da gwamnatin Filaton ta fitar, gwamna Lalong ya ce bai yi kalaman ba domin muzanta kiristocin kasar.
Kwamishinan watsa labaran jihar, Mr. Dan Manjang ya tabbatar wa BBC cewa ba a fahimci kalaman da gwamnan ya yi ba.
'‘Maganar da gwamna ya yi shi ne fafaroma bai hana shi ba, ba wai nuna kaskanci ya yi masa ba, illa girmama shi wanda wasu mutane da yawancin kiristocin Najeriya suka yi wa mummunar fahimta'' In ji Dan Manjang.
A kan batun son raba kawunan kiristoci da kungiyar ke zargin gwamna Lalong kuwa, mista Dan Manjang ya ce ba dukkan kiristoci ne ke adawa da batun daukar musulmi da musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma mataimaki ba da jam’iyyar APC ta yi.
Karin bayani
Wannan takardamar dai ta samo asali ne daga wata hira da Gwamna Simon Lalong ya yi da manema labarai a fadar Shugaban kasa a ranar Laraba, inda ya ce nadinsa a matsayin daraktan Kamfe na jam’iyyar APC bai sabawa addininsa na kirista ba duk da cewa ‘yan takarar duka musulmi ne.
Da dama dai na ganin an nada shi ne domin rarrashin kiristoci a yankin arewacin kasar wadanda ke kallon matakin jam’iyyar mai Mulki na dauko Musulmi daga yankin a zaman dan takarar mataimakin shugaban kasa a maimakon kirista kamar yadda aka al’adanta a zaman cin fuska a gare su.