Me ya sa siyasar mata a duniya ke fuskantar koma-baya?

- Marubuci, Vibeke Venema, Stephanie Hegarty and Leoni Robertson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
- Lokacin karatu: Minti 6
Kusan rabin al'ummar duniya sun gudanar da zaɓuka a 2024, to amma an samu raguwar wakilcin mata a jagoranci.
A cikin kashi 60 na ƙasashen da suka gudanar da zaɓukan an samu raguwar wakilcin mata a majalisun dokokin ƙasashen.
A ƙasashen Indiya da Amurka da Faransa da Portugal da Afirka Kudu da sauran wasu ƙasashe 21, an samu raguwar wakilcin mata asabbin majalisun dokokin ƙasashen saɓanin tsoffin majalisun.
A karon farko a tarihinta an zaɓi adadi mafi ƙanƙanta na mata a majalisar Tarayyar Turai.
A wata ƙasar ma babu mace ko guda da ta samu kujera a majalisar dokokin.
Dakta Puakena Boreham ta kasance mace ta uku da ta taɓa zama 'yar majalisar dokokin ƙasar Tuvalu da ke yankin Pacific.
Ta shafe shekara takwas a matsayin mace ɗaya tilo a majalisar mai mambobi 16. Amma a wannan shekara ta rasa kujerarta.
A ƙarshen wa'adin mulkinta, ta shiga cikin gangamin neman yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska, domin mayar da wariyar jinsi babban laifi.
A wani ɓangare na gangamin, ta gudanar da jawabai a ɗakunan taruka, inda al'adance ba a barin mata su yi jawabai.
"Ina tunanin jawaban da na riƙa yi a matsayina na mace ne suka janyo min faɗuwa zaɓe," in ji Dakta Boreham.
"Na ji takaici a lokacin da na fahimci cewa mata ba za su samu wakilci a majalisa ba a tsawon shekara huɗu masu zuwa''.
Tuvalu wadda ke tsibirin Pacific ta ƙasance ƙasar da mata ke da ƙarancin wakilci a majalisa.
Mata sun samu ƙarin wakilci a ƙasashen Birtaniya da Mongolia da Jordan da kuma Jamhuriyar Dominican , yayin da a karon farko ƙasashen Mexico da Namibia suka zaɓi mata a matsayin shugabanninsu.
A yanzu yankin Latin da Afirka na kan gaba.
Amma tun lokacin da aka zaɓi mace ta farko a matsayin 'yar majalisa a Duniya a ƙasar Finland a 1907, ƙudirin daidaiton wakilci ke raguwa.
Tsakanin 1995 zuwa 2020, an samu ninkuwar wakilcin mata a faɗin duniya, to amma an fi samu jan ƙafa dangane ƙudirin cikin shekara uku da suka gabata.

A wasu ƙasashe irin su Portugal da Pakistan da Amurka adadin mata 'yan siyasa na raguwa, yayin da majalisun dokokinsu ke ƙara komawa hannun masu ra'ayin riƙau.
Galibi jam'iyyun masu ra'ayin riƙau a waɗannan ƙasashe mata ba su samun dama a cikinsu.
Ko a Birtaniya inda aka zaɓi ƙarin mata a majalisar dokokin ƙasar - akwai irin wannan matsalar, amma kuma aka samu akasin hakan.
A Faransa, zaɓin ƙasar bai yi wa mata 'yan takara mata daɗi ba.
"Idan akwai gagarumar zazzafar adawa, jam'iyyu ba su fiya bai wa mata takara ba,'' in ji Réjane Sénac, ƙwararriya a fannin kimiyyar siyasa da jinsi.

Asalin hoton, UNDP
A wasu ƙasashen mata na da wasu nauye-nauyen da ke kansu, fiye da maza, wanda kuma shi ke hana su shiga siyasa, in ji Rachel George, wata ƙwararriya kan siyasa da jinsi a jami'ar Stanford da ke Amurka.
Kuma hakan ya kawo musu cikas, kasancewa ba kowace majalisa ba ce ke bayar da hutun haihuwa.
Wasu Bincike da aka gudanar sun gano cewa mata kan sha wahala wajen samun kuɗaɗe yaƙin neman zaɓe ko kuma samun 'yancin kashe kuɗaɗe domin tayawa takara.
Haka ma binciken ya gano cewa a ƙasashe daban-daban ana samun ƙaruwar sukar mata kan rayuwarsu da shafukan intanet da ma a zahiri.
A shekarar da ta gabata an samu fitattun mata da suka janye jikinsu daga siyasa, suna masu bayar da dalilin cin zarafi.
A matsayinta na Sanata a Mexico, Indira Kempis ta ce ta sha fama da tsananin cin zarafin da ta ce takwarorinta maza ba sa fuskanta.
"An sha yi mini barazana, an cutar dani a siyasance, tare da cin zarafin iyalina.''
Wani mutum ya taɓa aike wa mijinta saƙo game da ita, a wani mataki da ta ce ya kusa harguza aurenta. An riƙa kiran dantinta a waya ana yi musu bazarana.
"Za su riƙa saka danginka a ciki, saboda sun san mu mata muna da rauni, abin ya cutar da ni ba kaɗan ba.''
A yanzu idan aka tambayeta game da shigar siyasar mata, ba ta iya magana.
"Ta yaya zan ƙarfafa wa mace gwiwa ta faɗa wannan matsala? Ta ya zan jefa ta a yaƙin da ba ta san yadda za ta kuɓuta ba.

Asalin hoton, Getty Images
"Maganganun banza da zage-zage da yarfe - waɗanan abubuwa sun zama ruwan dare a shafukan intanet," in ji Jang Hye-Yeong, wadda ta kasance ɗaya daga cikin mata 'yan majalisar Koriya ta Kudu, amma ta rasa kujerarta a bana.
"A duk lokacin da na bayyana a gidan talbijin, za a yi ta kiraye-kirayen waya, mutane su yi ta maganganu wa gidan talbijin ɗin, me ya sa za ku kawo mana mai rajin kare mata? in ji ta.
Lokuta da dama a yaƙin neman zaɓe idan tana magana kan abubuwan da suka shafi mata, kamar daidaito wajen albashi da cin zarafin lalata akan fuskanci dakatar da ita.
"Don haka na shirya wa tunkarar wannan barazana."

Asalin hoton, .
Jam'iyyar Jang ta samu koma-baya a wannan shekara, wani abu da ya taimaka wajen faɗuwarta zaɓe, amma ta ce gangaminta kan rajin kare mata ne babban abin da ya janyo mata faɗuwa.
Zaɓen bai kasance koma-baya ga mata a Koriya ta Kudu ba, domin an samu ƙaruwar adadin 'yan majalisa mata daga kashi 19 zuwa 20 cikin 100. Amma duk da haka ƙasar ba ta kai matsakaicin kashi 27 na duniya ba.
Ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da za a iya rage tazarar da ke tsakanin jinsi, ita ce ware wa kowane jinsi adadin kujeru, domin kuwa a yanzu ƙasashen da ba sa ware wa mata kujeru sukan zaɓi kashi 21 na mata a majalisa.
An ga yadda hakan ya yi tasiri ƙasar Mexico wadda ta ɓullo da wani tsari - a lokacin tsohon shugaban ƙasar Andrés Manuel López Obrador - da zai bai wa mata damar samun kashi 50 na kujerun majalisa.
Wani abu da ake ganin ya taimaka wa ƙasar zaɓen shugabar ƙasa mace ta farko (Claudia Sheinbaum), a wannan shekara.

Amma samun nasara rabin yakin ne, in ji Indira Kempis, wadda aka zaɓa amatsayin Sanata a 2018.
"Ni mace ce da ke son siyasa don na samu matsayi, nakan faɗi wannan saboda mata da yawa sukan ji kunyar hakan,'' in ji ta.
Akan nuna hana ta zuwa tarukan da ake yanke shawarwari. ''Dole na tilasta w akaina shiga ciki. siyasa ta kasance tamkar ƙungiyar maza.
Ta kuma takan fuskanci tsangama daga takwarorinta maza a koyaushe.
Jang na shirin sake tsayawa takara a Koriya ta Kudu, haka ma Puakena Boreham a Tuvalu.
"Ko da ban samu nasara, dole a ji murya mata a ciki,'' in ji ta.











