Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗaukar cikin wata 15: Yadda ake damfarar masu neman haihuwa ido rufe
- Marubuci, Yemisi Adegoke, Chiagozie Nwonwu da Lina Shaikhouni
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 8
Chioma ta dage kai da fata cewa Hope, jaririn da take riƙe da shi a hannunta, ɗanta ne. Bayan shekaru takwas na yunƙurin samun ciki, tana ganin shi a matsayin ɗanta da ya zo gare tamkar wata kyauta daga Allah.
"Wannan jaririn nawa ne," in ji ta cikin turjiya.
Tana zaune kusa da mijinta, Ike, a ofishin wata jami'ar gwamnatin Najeriya wadda ta shafe kusan sa'a guda tana yi wa ma'auratan tambayoyi.
Ify Obinabo a matsayinta ta kwamishiniyar harkokin mata da walwalar al'umma a jihar Anambra, tana da ƙwarewa sosai wajen warware rikicin iyali – amma wannan ba irin taƙaddamar da aka saba gani ba ne.
Dangin Ike, su biyar, waɗanda su ma suna cikin ɗakin, ba su amince da cewa Hope ɗan ma'auratan ba ne.
Chioma ta yi iƙirarin ta “ɗauki” cikin yaron na kusan wata 15. Kwamishiniyar da iyalan Ike sun kasance cikin tababa.
Chioma ta ce ta fuskanci matsin lamba daga dangin Ike saboda rashin samun ciki. Har ta kai ga sun neme shi ya ƙara aure.
A cikin ɓacin rai, ta ziyarci wani “asibiti” inda ake ba da wani “magani” ba irin wanda aka saba da shi ba - wata zamba mai ban tsoro da tayar da hankali da ta shafi fataucin jarirai inda ake damfarar mata masu matuƙar buƙatar haihuwa.
Mun sauya sunayen Chioma da Ike da sauran mutanen da ke cikin wannan labarin don kare su daga abin da zai iya biyo baya daga al'ummarsu.
‘Aikin ƴan baiwa’
Najeriya na daga cikin ƙasashen da aka fi yawan haihuwa a duniya, inda mata sukan fuskanci matsin lamba a cikin al'umma don su ɗauki ciki har ma da kyama ko cin zarafi idan ba su haihu ba.
Sakamakon wannan matsin lamba, wasu matan kan wuce gona da iri don tabbatar da burinsu na zama iyaye.
Sama da shekara guda, BBC Africa Eye tana binciken badakalar "ɗaukar cikin ɓoyi".
Ƴan damfara da ke bayyana kansu a matsayin likitoci ko ma'aikatan jinya sun yaudari mata cewa suna da "maganin haihuwa mai kamar mu'ujiza" inda suke da tabbacin samun ciki. A karon farko na “Maganin” sai an biya ɗaruruwan daloli kuma ya ƙunshi allura da wani abin sha, ko wani abu da ake turawa a cikin al'aura.
Babu ɗaya daga cikin mata ko jami'an da muka zanta da su yayin bincikenmu da ya san haƙiƙanin abin da ke cikin waɗannan magunguna. Amma wasu matan sun shaida mana cewa sun haifar da sauye-sauye a jikinsu - kamar kumburin ciki - wanda hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa suna da juna biyu.
Akan gargaɗi matan da aka bai wa "maganin" da kada su ziyarci kowane likita ko asibiti da daban, saboda babu wani bincike ko gwajin ciki da zai iya gano "jaririn", wanda masu zamba suka ce yana girma ne a wajen mahaifa.
Idan lokacin ''haihuwa'' ya yi, ana faɗa wa matan cewa ba za su fara naƙuda ba sai sun sha wasu ''magunguna'' masu tsada , wanda ke nufin sai sun ƙara biyan wasu kuɗaɗe.
Labarin yadda ''haihuwar'' ke faruwa ya bambanta, amma duk suna da tayar da hankali. Wasu ana yi masu allurar barci ne kawai sai da su farka su ga alamar yanka kamar an yi masu fiɗa. Wasu kuma sun ce an yi musu allurar da ke gusar da hankulansu su faɗa cikin yanayin maye inda za su ga kamar cewa suna haihuwa.
A ƙarshe dai matan na samun jariran da suka yi amannar cewa su suka haifa.
Chioma ta shaida wa kwamishiniyar Iafiya cewa da lokacin ''haihuwarta'' ya yi, wanda ake kira likitan ya yi ma ta allura a kwankwaso ya ce ta yi nishi. Ba ta fayyace yadda ta ƙare da Hope a hannunta ba, amma ta ce haihuwa na da ''zafi''.
Tawagarmu ta yi nasarar kutsawa ɗaya daga cikin waɗannan "asibitocin" na sirri - domin ganawa da wata mata, wadda abokan hulɗarta ke kira "Dakta Ruth" - inda ma'aikatanmu suka yi ɓadda-bami da cewa su ma'aurata ne da suka kwashe shekara takwas suna neman haihuwa.
Wannan mata mai suna “Dakta Ruth” tana gudanar da asibitinta ne a duk ranar Asabar ta biyu na kowanne wata a wani dagargajajjen otal da ke garin Ihiala a jihar Anambra. A wajen ɗakinta na otal ɗin, mata da dama ne ke jiran ta, wasu na ɗauke da ciki kamar juna-biyu.
Mutane na ta kai-komo a wurin cikin kyakkyawan fata. An yi murna sosai a cikin ɗakin lokacin da aka sanar cewa wata mata tana ɗauke da juna biyu.
Lokacin da ƴan jaridarmu na sirri suka shiga ganin ta, "Dakta Ruth" ta faɗa musu cewa tabbas maganin yana aiki.
Ta yi wa matar tayin wata allura, tana mai cewa hakan zai ba wa ma'aurata damar "zaɓen" jinsin abin da za a haifa - wani abu da ba mai yuwa ba ne a likitance.
Bayan sun ƙi karɓar allurar, “Dakta Ruth” ta miƙa musu ledar garin magani da kuma wasu ƙwayoyin da za su sha a gida, tare da bayanin lokacin da za su yi jima’i.
A karon farko za su biya naira 350,000 (sama da $200).
Wakiliyarmu da ta yi basaja ba ta sha magungunan ba kuma ba ta bi umarnin "Dakta Ruth" ko ɗaya ba, amma ta dawo wurinta bayan makonni huɗu.
Bayan ɗora na'urar da ke kama da na'urar daukar hoton ɗan tayi a tumbin wakiliyar BBC, an ji sauti kamar bugun zuciya kuma "Dakta Ruth" ta taya ta murna da samun juna biyu.
Dukkansu suka ɓarke da murna.
Bayan faɗa musu hakan, “Dakta Ruth” ta buƙace su su sayi wani magani 'mai wahalar samu' kuma mai tsadar gaske, wanda ake buƙata kafin a iya haihuwar jinjirin, wanda kuɗinsa ya kai naira miliyan ɗaya da rabi zuwa miliyan biyu ($1,000).
'Dakta Ruth' ta ce idan ba tare da wannan maganin ba, ciki zai iya wuce watanni tara, ba tare da la'akari da batun kimiyya ba, ta ƙara da cewa: Ɗan tayin zai yi fama da rashin abinci mai gina jiki - muna buƙatar sake gina shi."
"Dakta Ruth" ba ta mayar da martani kan zarge-zargen da BBC ta yi ma ta ba.
Ba a fayyace iyakar yadda matan da abin ya shafa suka yi amanna da wannan ikirari ba.
Amma ana iya ganin alamun dalilan da za su sanya su iya amincewa da irin waɗannan ƙarairayi idan aka bincika shafukan sada zumunta na Intanet inda ake yaɗa bayanan ƙarya kan batun samun ciki da kuma haihuwa.
Kafafen yaɗa bayanan ƙarya
Ɓoyi wani ciki ne da aka sani a likitance, wanda mace ba ta da masaniya kan cewa tana da juna biyu har sai cikin yayi nisa.
Sai dai a yayin da muke gudanar da bincike, BBC ta gano yadda ake yaɗa bayanan ƙarya kan irin wannan ciki a wasu shafukan dandalin Facebook.
Wata mata daga Amurka, wadda ta mayar da shafinta ya zama na batun kwantaccen ciki zalla, ta yi iƙirarin cewa tana da juna biyu “tsawon shekaru” kuma kimiyya ba za ta iya bayyana wannan lamari ba.
A cikin wasu shafukan Facebook, yawancin sakonnin da ake wallafawa suna amfani da kalmomin addini ne wajen yabawa wannan "maganin" na bogi a matsayin "abin al'ajabi" ga waɗanda suka kasa yin ciki.
Duk waɗannan bayanan na ƙarya suna taimakawa wurin dulmuyar da mata ya kai su ga amnicewa da wannan zamba.
Nutanen da ke cikin waɗannan ƙungiyoyi ba daga Najeriya kaɗai suke ba, har ma daga Afirka ta Kudu da yankin Caribbean, har ma da Amurka.
Su kuma mazambatan suna amfani da su don ƙara faɗaɗa kasuwarsu.
Da zarar wani ya bayyana shirye-shiryen fara zambar, ana gayyatar su zuwa ƙungiyoyin WhatsApp na sirri. A can, masu gudanar da shafukan suna yaɗa bayanai game da "asibitocin sirri" da abin da tsarin ya ƙunsa.
'Har yanzu a rikice nake'
Hukumomi sun shaida mana cewa don cika wannan damfara tasu, mutanen na buƙatar jarirai sabbin haihuwa, kuma domin samun hakan sukan nemo matan da ke cikin tsanani ko waɗanda ke cikin wahala, musamman ƴanmata masu juna biyu, kasancewar zubar da ciki haramun ne a ƙasar.
A watan Fabarairun 2024, ma'aikatar lafiya ta jihar Anambra ta kai samame wurin da Chioma ta ''haifi'' Hope.
BBC ta samu hotunan harin, wanda ya nuna wani katafaren gini da ya ƙunshi gine-gine biyu.
A ɗaya akwai ɗakuna ɗauke da kayan aikin likita - wanda ake amfani da su kan marasa lafiya - yayin da a ɗaya kuma akwai mata masu juna biyu da aka ajiye ba tare da son ransu ba. Wasun su ba su wuce shekaru 17 ba.
Wasu sun faɗa mana cewa an yaudare su ne su suka je wurin, ba tare da sanin cewa an sayar da jariransu ga abokan cinikin ƴan damfarar ba.
Wasu kuma kamar Uju, wadda ba sunanta na asali ke nan ba, sun ji tsoron faɗa wa danginsu cewa suna da juna biyu kuma sun nemi mafita. Ta ce an ba ta naira 800,000 (kusan dala 500) kan jaririn.
Da aka tambaye ta ko ta yi nadama game da shawarar da ta yanke na sayar da jaririnta, sai ta ce: “Har yanzu a rikice nake.”
Kwamishiniya Obinabo, wadda ta kasance da hannu a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi a jiharta na daƙile wannan badaƙala, ta ce masu damfarar mutane suna harin mata masu rauni irin su Uju domin samo jariran.
Bayan ta kammala yi ma ta tambayoyi, kwamishina Obinabo ta yi barazanar karɓe jariri Hope daga wurin Chioma.
Amma Chioma ta roƙi afuwa, tana mai jaddada cewa ita kanta abin ya shafa kuma ba ta fahimci abin da ke faruwa ba.
Daga ƙarshe kwamishinar ta amince da hujjarta.
A yanzu, Chioma da Ike suna riƙe da jaririnsu - sai dai idan iyayensa na asali sun zo neman shi.
Amma idan har ba a sauya tunanin da ake yi kan mata, da rashin haihuwa da ƴancin haihuwa da kuma riƙon yara, zamba irin wannan za ta ci gaba da bunƙasa, in ji masana.