Ko Indiya ka iya zama babbar ƙasa me faɗa-a-ji a duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
A ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu, Indiya za ta fara shirye-shiryen babban zaɓe wanda zai ɗauki makonni shida kuma mutane miliyan 969 ne suka cancanci kaɗa kuri'a.
Firaminista Narendra Modi da jam'iyyarsa ta Bharatiya Janata Party (BJP) za su nemi wa'adi na uku a kan karagar mulki.
Indiya dai na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da suka mallaki makamin Nukiliya tare da isar kumbonta a duniyar wata.
Kuma tun bayan zaɓen gama-gari na karshe a shekarar 2019, ta zama ƙasa mafi yawan al’umma a duniya, inda ta wuce Ingila a matsayin ƙasa ta biyar mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Mutane da yawa na hasashen cewa Indiya za ta zama ƙasa mai karfin faɗa-a-ji a duniya amma hakan ya gamu da taka tsantsan.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasa mafi saurin bunƙasar tattalin arziƙi
"Indiya za ta zama injin ci gaban duniya," in ji Mista Modi yayin wata ziyara da ya kai Afirka ta Kudu a watan Agustan da ya gabata.
Har zuwa ƙarshen shekarar 2023, ƙasar ta tabbatar da kambunta a matsayin ƙasa mafi saurin bunƙasar tattalin arziki a duniya bayan da ta ƙaru da kashi 8.4 cikin 100 a cikin watanni ukun karshe na shekara.
Ana iya auna tattalin arziƙin duniya da kuɗaɗen da ƙasa ke samu wato GDP wanda ke auna ayyukan tattalin arzikin kamfanoni da gwamnatoci da ɗaiɗaikun mutane a wata ƙasa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi, ciki har da bankin zuba jari na Amurka Morgan Stanley, Indiya ta kusan ta wuce Jamus da Japan wajen zama ƙasa ta uku mafi karfin tattalin arziki nan da shekarar 2027.
Wani abin mamaki shi ne kasancewar Indiya ƙasa ta ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya a shekarar 1947, lokacin da ta sami 'yancin kai.
Shekaru goma na mulkin Birtaniyya ya bar al'ummar ƙasar da rashin isassun kayayyakin more rayuwa da masana'antar noma da ta kasa ciyar da al'ummarta da ke ƙaruwa.
A wancan lokacin, iya tsawon rayuwar da mutum ke yi a Indiya ya kai shekaru 35. A yau kusan ya ninka zuwa 67, a cewar bankin duniya, yayin da matsakaicin rayuwa a duniya ya kai shekaru 71.
Indiya ita ce ƙasa ta 10 da ta fi fitar da kayayyaki a duniya, in ji bankin duniya.
Babban abin da ƙasar ke fitar wa shi ne man da aka tace da demon da magunguna.
Haɓakar tattalin arziƙin ta ya sami bunƙasa ne ta hanyar bunƙasa masana'antar sabis da bunƙasa fannin sadarwa da ta manhaja.
Sai dai masana tattalin arziki sun lura cewa duk da irin wannan bunƙasa da ƙasar ke yi, har yanzu tana fama da matsalar rashin ayyuka.
Wani taƙaitaccen bayani daga HSBC ya yi kiyasin cewa Indiya na buƙatar samar da ayyukan yi miliyan 70 a cikin shekaru goma masu zuwa yayin da yawan al'ummarta ke ƙaruwa, amma da wuya ta samar da fiye da kashi uku na hakan.

Ƙaruwar yawan jama'ar ƙasar

Asalin hoton, Getty Images
Indiya tana da yawan matasa musamman idan aka kwatanta da yawancin ƙasashen da suka ci gaba, tare da matsakaicin shekaru 28.7 a cikin 2022, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Saɓanin haka, matsakaicin shekarun ƙasar China ya kai shekaru 38.4, yayin da na Japan ya kai shekaru 48.6.
Masana tattalin arziki Bashar Chakravorti da Gaurav Dalmia sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 2030, yawan mutanen da za su kai shekarun aiki a Indiya zai haura biliyan ɗaya, saɓanin yadda ya tsaya a yanzu kan biliyan 1.4 wanda ke nuna gagarumin sauyin al'umma.
Sun tabbatar da cewa wannan rabe-raben alƙaluma ya kasance muhimmi wajen haifar da ci gaban tattalin arzikin da aka samu a sauran ƙasashen Asiya kamar Japan da China wanda ya dogara ga wannan "yawan waɗanda suka kai shekarun yin aiki.
Amma riƙe duk waɗannan ma'aikatan na iya zama da wahala. Indiya ce ke da mafi yawan 'yan kasar da ke zaune a ƙasashen waje - kusan miliyan 18, a cewar MDD.
Kusan mutane miliyan 2.5 suna ƙaura zuwa ƙasashen waje a kowace shekara, gami da wasu daga cikin manyan ƙwararrun masana ilimi.

Yawancin Indiyawan suna zaɓar zama a ƙasashen waje har abada, la'akari da alkaluma daga Ma'aikatar Harkokin Waje da ke ƙididdige adadin mutanen da suka yi watsi da zama ƴan ƙasar Indiya.
Ƙasar ba ta amince da mutum ya zama ɗan ƙasa biyu ba. A cikin shekarar 2022, fiye da mutum 225,000 sun soke ƴancinsu da damarsu na zama ƴan ƙasar Indiya, mafi girma cikin fiye da shekaru goma.
Ga yawancin mutanen da ke zaune a Indiya, neman aikin yi ya zama babban ƙalubale.
Kididdigar gwamnati ta sanya adadin rashin aikin yi a Indiya a kashi 8 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 3.8 cikin 100 a Amurka.
A cikin Maris, Ƙungiyar Kwadago ta Duniya ta ce mutane masu shekaru 15-29 sun kai kashi 83 cikin 100 na marasa aikin yi a Indiya inda mafi yawansu ke da aƙalla karatun sakandare.
"Na yi tafiya akai-akai a duk faɗin Indiya muna tattaunawa da matasa. Suna cikin baƙin ciki kuma ba su da sha'awar duk wani ra'ayi na mu'ujiza na Indiya," in ji ɗan jaridan Indiya kuma marubuci Siddhartha Deb, wanda littattafansa suka mayar da hankali kan haɓakar Indiya.
"Ci gaban tattalin arziki ya kawo sabbin ababen more rayuwa kamar manyan tituna da filayen jirgin sama, kuma adadin masu kuɗi ya karu. Amma mutane a Indiya gaba ɗaya suna ƙoƙawa," in ji shi.
Ina mata ma'aikata suka shiga?

Asalin hoton, Getty Images
Kashi 33 cikin 100 na mata masu aiki ya yi ƙasa a cewar gwamnati idan aka kwatanta da kashi 56.5 cikin 100 a Amurka da kashi 60.5 a China da matsakaicin duniya na kashi 49, in ji bankin duniya.
Yayin da yawancin matan Indiya a baya ake musu aure kuma su zama matan zaman gida, da yawa yanzu na neman ilimi.
Farfesa Ashwini Deshpande, masaniya kan tattalin arziki a jami'ar Azim Premji da ke Bangalore, ta ce mata da yawa masu aiki suna sana'o'in dogaro da kai ne, wanda hakan na iya jefa su cikin mawuyacin hali.
"Akwai buƙatar gaggawa don ƙara shigar da mata cikin ma'aikatu domin yin aikin da za a biya su albashi na yau da kullun tare da kwangilolin aiki da fa'idojin tsaro," in ji ta.
Ana ci gaba da nuna bambanci da rashin daidaito

Asalin hoton, Getty Images
Indiya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ba su da daidaito da kuma nuna bambanci a duniya.
Kusan rabin al'ummar ƙasar na rayuwa ne a kasa da dalar Amurka 3.10 a rana, tsaka-tsakin talauci na Bankin Duniya, yayin da adadin attajiran Indiya ya tashi daga mutum ɗaya a shekarar 1991 zuwa 162 a shekarar 2022, a cewar Mujallar Forbes.
Yayin da masu matsakaicin matsayi ke faɗaɗa, "akwai rashin daidaito sosai a Indiya", a cewar Dr Ashoka Mody, farfesa a manufofin tattalin arziki na ƙasashen duniya a Jami'ar Princeton a Amurka.
"Kuma wannan yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa ya zama wauta a ɗauka cewa Indiya za ta zama ƙasa mai ƙarfi ba tare da manyan canje-canjen tsarin ƙasar ba."
Ɗaya daga cikin sauye-sauyen da ake buƙata, in ji Dokta Mody, shi ne gyara a ɓangaren zamantakewa da ke magance wannan rashin daidaito, ciki har da karfafa tsarin kiwon lafiyar jama'a na Indiya.
"Ga ɗaruruwan miliyoyin Indiyawa, da wahala samun ayyukan yi, kuma ɓangaren ilimi da kiwon lafiya su ma sai a hankali."
Rarrabuwar kai ta siyasa na ƙaruwa

Asalin hoton, Getty Images
Rarrabuwar kai a siyasa ba sabon abu ba ne a Indiya. Tun daga shekarun 1800, ƙasar ta yi ta muhawara kan ko ya kamata ta zama al'ummar da ba ruwanta da addini ko Hindu - kusan kashi 80 na al'ummar ƙasar Indiya sun kasance mabiya addinin Hindu.
Tattaunawa ta tsananta bayan nasarar da jam'iyyar BJP ta Hindu mai kishin kasa ta Mr Modi ta samu a shekarar 2014.
Al'amura na nuna kyama ga Musulmai sun karu kuma a cikin watan Maris, Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin Amurka sun bayyana damuwarsu game da zartar da wata doka da ta saukaka wa tsirarun addinai waɗanda ba Musulmi ba daga Pakistan, Bangladesh da Afghanistan neman zama ƴan kasa.

Asalin hoton, Getty Images
Marubuciya Devika Rege, wadda kwanan nan ta buga Quarterlife, labari mai cike da ce-ce-ku-ce game da Indiya a sakamakon zaɓen 2014, ta yi imanin cewa ƙasarta na fuskantar babban "rashin jituwa tsakanin al'umma".
"Yana da wuya a musanta karuwar cigaban Indiya, amma an tauye 'yancin walwala da kuma rashin jituwa tsakanin al'umma."
Indiya ba ta kasancewa yadda ƙasashen yamma ke so

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru da dama, ƙasashen yammacin duniya sun yi fatan Indiya za ta zama mai daidaita karfi da ƙasar China a Asiya. Kazalika kasancewarta kasa mai makaman nukiliya, ita ma tana da rundunar tsaro ta biyu mafi girma a duniya da ke da jami'ai miliyan 1.45.
Amma ba akoyaushe Indiya ke kasancewa yadda ƙasashen yamma ke so ba.
A cikin shekaru biyu da suka gabata Indiya ta sha suka kan matsayinta a yaƙin Rasha da Ukraine da kuma sayen mai na Rasha a farashi mai rahusa duk da takunkumin da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa Moscow.
Saniya Kulkarni, kwararriya kan hulɗar ƙasashen duniya a Makarantar Koyon Tattalin Arziki da Kimiyyar Siyasa ta Landan, ta ce ƙasashen Yamma za su iya sa ran Indiya ba za ta zama "masu wayo" kamar China ba amma ta yi gargaɗin cewa tana da nata burin.
"Ba zai yi kyau a yi tsammanin Indiya za ta yi aiki a matsayin jakada ga Yamma ba," in ji ta. "











