Ko Tinubu ya karya dokar Najeriya ta hanyar tura sojoji Benin?

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP via Getty Images
A ranar Talata ne Majalisar dattijan Najeriya ta amince wa Tinubu ya tura dakarun ƙasar zuwa Jamhuriyar Bnenin.
Shugaban Bola Tinubu ya buƙaci tura dakaru Benin ne domin tabbatar da zaman lafiya sanadiyyar yunƙurin juyin mulki da aka samu a ƙasar cikin wannan mako.
A ranar Lahadi ne wasu sojoji suka bayyana a kafar talabijin ta Jamhuriyar Benin inda suka bayyana cewa sun tuntsurar da gwamnatin ƙasar.
Gungun sojojin ƙarƙashin jagorancin Pascal Tigri, sun so ne su haɓarar da gwamnatin Patrice Talon wanda yake jagorantar ƙasar tun daga watan Afrilun 2016.
Sai dai daga baya hukumomin Jamhuriyar Benin sun fito sun bayyana cewa an tarwatsa shirin masu juyin mulkin.
Najeriya ta bayyana cewa ta bayar da gudumawa wajen ganin an daƙile yunƙurin masu juyin mulkin.
Bayan gwamnatin Jamhuriyar Benin ta tabbatar da cewa an daƙile shirin masu juyin mulki, wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ta ce sojojin Najeriya sun kai ɗaukin gaggawa game da batun juyin mulkin.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan samun buƙatar hakan daga gwamnatin Benin, inda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jiragen yaƙin Najeriya su karɓe iko da sararin samaniyar Benin tare da korar masu yunƙurin juyin mulki daga tashar talabijin ta ƙasar da kuma wani sansanin soji.
Abin da ya sa Tinubu ke son tura sojoji Jamhuriyar Benin

Asalin hoton, STUART PRICE/AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin takardar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura wa Majalisar Dattijai, ya ce akwai buƙatar gaggawa ta taimaka wa Jamhuriyar Benin kan halin da ta fada a ciki.
Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar da Bola Tinubu din ya tura wa Majalisar ta buƙatar tura sojojin zuwa Benin.
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa "wannan buƙata ta taso ne a matsayin ɗori kan buƙatar da aka samu daga gwamnatin Jamhuriyar Benin ta buƙatar tallafin tallafin gaggawa daga sojojin saman Najeriya."
"Ya kamata majalisar dattijan Najeriya ta sani cewa Jamhuriyar Benin a halin yanzu na fuskantar ƙalubale na yunƙurin ƙwace iko da kuma tarwatsa dimokuraɗiyya," kamar yadda Tinubu ya faɗa a cikin wasiƙarsa.
Tinubu ya ce halin da ake ciki a Jamhuriyar Benin na buƙatar 'ɗauki daga ƙasar waje aikin gaggawa', shi ya sa ake buƙatar tura dakaru zuwa ƙasar.
"Saboda ƴan'uwantaka da abokanataka da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin, nauyi ne a gare mu tallafa wa Jamhuriyar Benin bisa buƙatar da ta gabatar."
Me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce?
Sashe na biyar na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce babu wani jami'in sojin Najeriya da za a tura aiki a wata ƙasa ta daban face da amincewar majalisar da dattijan ƙasar.
Sai dai sashen ya ya kuma bai wa shugaban Najeriya ƙarfin iko tura sojoji zuwa wata ƙasa idan ya yi tunanin akwai wata barazana.
Sashe na 5 (ƙaramin sashe na 4(b)) ya ce "face da amincewar majalisar dattijai, babu wani jami'in sojin tarayyar Najeriya da za a iya turawa yaki a wata ƙasa."
Ƙaramin sashe na biyar kuma ya ce "...shugaban ƙasa, tare da Majalisar Tsaro ta ƙasa, na iya tura dakarun Najeriya domin ƙaddamar da ƙwarya-ƙwaryar aiki a wajen Najeriya idan suka gamsu cewa babu makawa tsaron Najeriya na cikin hatsari."
Kundin tsarin mulkin Najeriyaajeriya ya ƙara da cewa shugaban ƙasa zai iya neman izini cikin kwana bakwai gabanin tura sojoji, kuma majalisar dattijan na da tsawon mako biyu ta amince ko kuma ta ƙi amincewa.

Asalin hoton, @Reportercd1/X
Tun shekarar 1991 da Jamhuriyar Benin ta koma bin tafarkin dimokuradiyya, an samu yunƙuri daban-daban na juyin mulki waɗanda ba su yi nasara ba.






