Akuya mafi tsayin kunne ta yi farin jini a duniya

Simba's ears being held up by his proud owner - Pakistani goat breeder Mohammad Hasan Narejo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai akuyar Mohammad Hasan Narejo ya rike kunnuwan akuyar tasa Simba cikin alfahari

Kusan kowa ya san labarin Dumbo, wata giwa a wani shirin talabijin na barkwanci mai fala-falan kunnuwa da har abokan wasanta ke tsokanarta.

A yanzu ba wannan giwar ce kadai dabbar da ke da manyan kunnuwa ba.

Ga wata akuya ma mai suana Samba da aka haifa a birnin Karachi na Pakistan, wacce tsayin kunnuwanta suka kai santimita 54.

Sai dai a yanzu lokaci ya sauya abubuwa. Maimakon a dinga tsokanar Simba, sai ta zamo wata tauraruwa mai farin jini a duniya.

Akuyar mallakin wani mutum ne Mohammad Hasan Narejo, wanda ya shaida wa AFP cewa ya nemi shirin Guiness Book of Record da ya sanya akuyar a kundin adana abubuwan ban mamaki na duniya.

Yana so a sanya ta ne a matsayin "Akuyar da babu irin ta a zamanin nan".

Har yanzu ba a bayyana ko a wane rukuni akuyar ta faɗa ba, don haka babu tabbas kan ko tsayin kunnen Simba na iya shiga kundin tarihi na Guiness.

Sai dai ko a saka ta ko kar a saka ta, tuni akuyar ta samu tagomashi da farin jini a Pakistan, bayan da aka fara yaɗa hotunan fala-falan kunnuwanta.

Amma kuma a ɓangaren akuya Simba, waɗannan dogwayen kunnuwa na iya zame mata ƙalubale.

Sometimes Simba trips on his own ears, forcing his owner to be creative with solutions

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu lokutan Simba kan take kunnuwanta, har su harɗe ta

Alal misali, tsayin nasu na iya zame mata barazana,

Don hana afkuwar wani mummunan abu, sai Mista Narejo Narejo yake ɗaure mata kunnuwan a wuyanta.

Wata fargabar ita ce ta wasu makiyayan abokan hamayya, waɗanda halayyar da suke nuna wa kan akuyar ke damun Mr Narejo.

Yanzu ya mayar da hankali kan tsananta addu'a da ɗaukar matakai don hana magabta cutar da ita.

"Muna karanta ayoyin kur'ani mu tofa mata don neman kariya daga kambun baka," kamar yadda ya shaida wa AFP.

A hannu guda kuma yana da dogwayen burika.

Yana so ya kiwata Simba ta hanya mai inganci kuma ya zama gwarzo wajen kiwon dabbobi a Pakistan.

"Dole sunan Simba ya karaɗe duniya," in ji shi.

Simba's ears continue to grow, including by a further 6cm (2.4in) in the past three weeks

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Simba na ci gaba da yin tsayi, inda ya ƙaru da santimita a mako ukun da suka gabata