An gano bakin akwatin da ke nadar bayanai na jirgin saman Amurka da ya yi hadari

Tarkacen jirgi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

An gano bakin akwatin da ke nadar bayanan abubuwan da suka faru a lokacin da jirgin fasinjan Amurka ya yi hadari.

Yanzu haka jami'ai sun dukufa domin gano abin da ya janyo jirgin ya yi taho mu gama da wani jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a yayin da ya ke kokarin sauka.

An bayyana alamun tambaya akan adadin ma'aikatan da suke kan aiki musamman wadanda ke kula da saukar jirage a lokacin da jirgin ya yi hadari.

Yawanci dai mutum biyu ne kan kula da yadda jirage ke sauka bisa la'akari da cewa filin jirgin na da cunkoson jiragen da ke tashi da sauka, shi ya sa dole sai an samu masu kula sosai wadanda zasu rika magana da matuka jiragen da ke tashi da sauka don basu damar sauka idan sun lura da babu cunkoso a sama ko kuma a kasa na jirage masu tashi.

Ana nuna shakku a kan ma'aikatan da ke aiki a lokacin inda ake zargin mutum guda ne a wajen ke aiki maimakon mutum biyu.

Bakin akwatin zai taimaka wajen gano abin da ya faru a lokacin hadarin da kuma saukakawa masu bincike aikinsu.

An yi amanna mutum 67 da ke cikin jiragen biyu sun mutu.

Jiragen sun yi taho mu gama ne yayin da suke dab da sauka a filin jirgin saman Reagan da ke Washington DC.

Mahukunta a Amurka sun ce za a kammala tattara dukkan bayanan da suka dace a game da hadarin jiragen a cikin kwanaki 30.

Shugaba Trump ya dora alhakin hadarin jirgin fasinjoji da ya yi taho mu gama da jirgin soji a kogin Potomac kan manufofin daukar aikin Amurka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wajen wani taron manema Labarai, Mista Trump ya ce ya yi amanna cewa an dauki wadanda basu cancanta bane aikin kula da zirga-zirgar jiragen ƙasar.

Sai dai bai bada shaidar da ta tabbatar da hakan ba.

Trump ya ce jirgin sojin ya bi ta inda bai dace ba a kuma lokacin da bai dace ba

An dai gano gawarwaki 30, to amma masu iyo a ruwa na ta kokari domin ganin an gano sauran gawarwakin mutanen da ke cikin jiragen biyu.

Filin jirgin sama Reagan dai ya kasance inda jirage ke yawan tashi da sauka abin da wasu ke alakanta hadarin da cunkushewar sararin samaniya a yayin da jirgin fasinja da kuma mai saukar ungulun da sojojin Amurka ke ciki ke kokarin sauka.

Jirgin helikoftan da ke dauke da sojoji uku a cikinsa na yin wani atisaye ne a lokacin da lamarin ya afku.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman na Reagan na wani lokaci lamarin da ya janyo fasinjojin suka yi jungum-jungum suna jiran lokacin da za a kira su don tafiya inda za su je.

Yanzu dai al'amura sun komai dai-dai a filin jirgin saman na Reagan.