Waiwaye: Batun fitar da takardun binciken Tinubu da damfarar kuɗi a tsarin CBEX

Asalin hoton, Nigeria Presidency
A farkon makon, labarin da ya fara jan hankalin mutane shi ne batun hukuncin wata kotu a Amurka da ta buƙaci hukumomin ƙasar su fitar da takardun sakamakon binciken Shugaban Najeriya Bola Tinubu wanda ya jawo sabon ce-ce-ku-ce kan rayuwarsa a Amurka.
Tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wasu ƴanjarida da kuma masu adawa da takarar Tinubu suka tono labarin da ke cewa hukumomin Amurka sun taɓa binciken shi kan ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, har ma aka ƙwace masa wasu kuɗaɗe a shekarun 1990.
A ranar 8 ga watan Afrilu ne wata kotun Gundumar Columbia da ke Amurka ta bai wa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) da kuma kuma hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (DEA) umarnin su fitar da bayanan binciken da suka gudanar kan Tinubu shekaru 30 da suka wuce.
Yadda aka kashe fiye da mutum 50 a Filato

Asalin hoton, @CalebMutfwang
Haka kuma a cikin makon an sake kashe aƙalla mutum 50 a wani hari da wasu ƴan bindiga suka a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Hukumomin gwamnatin jihar ta Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Karamar hukumar ta Bassa.
Mai bai gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro Admiral Shipi Gakji mai ritaya ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe "ya zarce 40."
Cika shekara 11 da sace ƴanmatan Chibok

Abu kamar wasa, Talata 15 ga watan Afrilun nan ne 'yanmatan sakandare ta Chibok ke cika shekara 11 a hannun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.
A irin wannan rana ne a shekarar 2014 'yanbindigar ɗauke da makamai suka afka makarantar da ke da nisan kilomita kusan 125 daga birnin Maiduguri na jihar Borno, inda suka sace yaran 276 da tsakar dare.
Satar ɗaliban ce irinta ta farko da aka taɓa gani a Najeriya, kuma tun daga lokacin 'yanbindiga suka mayar da abin sana'a.
Ganawar su Kawu Sumaila da Ganduje

Asalin hoton, Twitter
Wasu 'yanmajalisar tarayya na jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano sun bayyana dalilin wata ziyara ta musamman da suka kai inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Ƴanmajalisar sun haɗa da Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da danmajalisar wakilai Hon Kabiru Alhassan Rurum da danmajalisa mai wakiltar Dala Ali Madaki da tsohon dan majalisar tarayya wakilai Badamasi Ayuba.
A tattaunawar da ya yi da BBC bayan ganawar da suka yi da shugaban jam'iyyar ta APC, Kabiru Alassan Rurum, ya ce sun yanke shawarar kai wa Ganduje ziyarar ne wadda ya ce ta musamman ce bisa matsayinsa a kasa da kuma kasancewarsa jigo daga jihar da suke wakilta a tarayya wato Kano.
Damfarar kuɗin ƴan Najeriya ta tsarin CBEX

Asalin hoton, @cbex_official
Asarar kuɗi da ƴan Najeriya suka takfa a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX ya ja hankali a ƙasar, musamman a kafofin sadarwa.
Wannan matsalar ta zo ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar suke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa da rashin kuɗi, wanda ya biyo bayan janye tallafin man fetur da karyewar darajar naira.
Rahotanni sun ce kuɗin da ƴan Najeriya suka yi asara a tsarin na CBEX sun haura naira tiriliyan ɗaya, wanda hakan ya sa wasu suke mamakin yadda ƴan ƙasar suka iya tara maƙudan kuɗi haka cikin ƙanƙanin lokaci.
Ƴansanda sun ceto yaran da ake zargin ana safararsu zuwa ƙasashen waje

Asalin hoton, Getty Images
A cikin makon jiya ɗin ne dai rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar kuɓutar da wasu yara ashirin da uku daga wani gidan marayu da ke Unguwar Kubwa a Abuja, babban birnin ƙasar wanda ake zargin ana fakewa da shi ana hada-hadar safarar yaran har zuwa ƙasashen waje.
Cikin yaran dai har da 'yan shekara ɗaya zuwa uku, wasun su kuma sun kwashe kimanin shekara uku a gidan.
DSP Mansir Hassan, shi ne jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriyar a jihar Kaduna, ya ce jami'an rundunar sun karaɗe jihohi goma sha ɗaya a ƙoƙarin bankaɗo gidan da kamo wadan da suke da hannu a satar yara, tare da hadahadar siyar da su.
Yadda ƴanbindiga suka yi garkuwa da kusan mutum 50 a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma duk a cikin makon dai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mazauna garuruwan Banga da Gidan Giji da sauran su da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, na ci gaba da barin garuruwan nasu sakamakon jerin hare-haren da ƴanbindiga ke ci gaba da kai musu.
A farkon makon nan ƴanfashin dajin sun kashe aƙalla mutum biyu tare da yin garkuwa da ƙarin wasu hamsin, waɗanda suka haɗa da maza da mata, inda suka buƙaci sai an biya su kuɗin fansa kafin su sako su.
Mazauna garuruwan Banga da Gidan Giji dai sun ce maharan da suka kai musu hari sun mamaye garinsu, tare da karin wasu garuruwa da dama wanda hakan ya tilastawa wasu tserewa saboda kaucewa harin yan bindigar.
Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga allunan yaƙin neman zaɓen 2027

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook
Haka kuma a farkon makon ne fadar gwamnatin Najeriya ta nesanta kanta daga allunan da ake yaɗawa a wasu biranen ƙasar na neman sake zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a shekarar 2027.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ba su da hannu a fitar da allunan, domin a cewarsa lokaci bai yi ba.
"Fadar shugaban ƙasar tana takaicin yadda ake ta yaɗa allunan neman zake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima na zaɓen 2027 musamman a titunan Abuja da Kano."











