Wakilan Rashford sun gana da Barca, Arsenal na son Sesko

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 1

Wakilan ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford sun gana da Barcelona, ​​Arsenal ta fara zawarcin ɗan wasan gaba na RB Leipzig Benjamin Sesko, Nottingham Forest ta shirya taya ɗan wasan Wolves Matheus Cunha.

Wakilan ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford sun gana da shugabannin Barcelona a ranar Talata yayin da dan wasan mai shekaru 27 ke neman hanyar ficewa daga Manchester United. (Sky Sports)

Arsenal ta yi wani bincike na wucin gadi a yunƙurin sayen ɗan wasan gaban Slovenia, Benjamin Sesko, mai shekara 21 daga kulob din RB Leipzig na Jamus. (Talksport)

AC Milan ta amince da yarjejeniyar sayen dan wasan bayan Ingila, Kyle Walker mai shekaru 34 daga Manchester City. (Sky Sports)

Dan wasan Manchester United Alejandro Garnacho ya fi son komawa Chelsea maimakon Napoli, wadda aka yi watsi da tayin da ta yi kan ɗan wasan na Argentina mai shekara 20. (TyC Sport)

Ita ma Napoli tana tattaunawa kan sayen ɗan wasan Jamus Karim Adeyemi mai shekaru 23 daga Borussia Dortmund. (Fabrizio Romano)

Juventus ta bai wa Chelsea damar sayen ɗan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 26, wanda kuma Manchester City da Arsenal ke zawarcinsa. (Teamtalk)

Ɗan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, na shawara kan inda zai koma, inda kungiyoyi da dama ke son ɗaukar sa. (ESPN)

Everton ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan Sporting na Ingila Marcus Edwards, mai shekara 26. (Cought Offside)

Wakilin ɗan wasan AC Milan Emerson Royal, mai shekara 26, ya tattauna da Everton da Fulham, amma kuma idon ɗan wasan bayan na Brazil yana kan Galatasaray. (Calciomercato)

Manchester United na tunanin ko za ta iya inganta tayin ɗan wasan Lecce Patrick Dorgu bayan an yi watsi da tayin farko na ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Denmark mai shekaru 20. (Star)

Sai dai Napoli na fatan doke Manchester United wajen ɗaukar Dorgu. (Gazzetta dello Sport)

Aston Villa da Newcastle United za su fafata kan ɗan wasan Ingila da AC Milan Fikayo Tomori mai shekaru 27. (Football Insider)