Matsayar ƴan majalisar Arewa kan ƙudirin haraji

Asalin hoton, Twitter
Ƴan majalisar dattawa daga shiyyar arewacin Najeriya sun buƙaci a dakatar da kudirin sabuwar dokar haraji da ke gaban majalisar da shugaban ƙasa ke neman amincewarsu.
Ƴan majalisar dattawan na arewacin Najeriya sun ce sun cimma wannan matsayar ne bayan tattaunawa tsakaninsu a ranar Litinin.
Wannan na zuwa bayan majalisar wakilai ta dakatar da duk wata muhawara da ta shafi kudirin dokar harajin bayan wakilan jihohin arewacin kasar a majalisar sun nuna adawa da kudirin dokar.
Ƴan majalisar sun cimma wannan matsaya ne bayan kudirin sabuwar dokar harajin ya tsallake karatu na biyu kuma aka miƙa shi gaban kwamitin kuɗi na majalisar domin sauraren bayanai daga kwararru.
Kudurin dokar harajin dai ya haifar da zazzafar muhawara a Najeriya da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar tarayya wanda ya ƙunshi manyan ɓangarori guda huɗu, domin neman amincewa.
Sai dai al'ummar arewacin kasar na ganin kudirin zai yi wa yankin illa, duk da gwamnati Bola Tinubu na cewa ba a fahimci kudirin dokar ba ne wanda ta ce idan aka amince zai daidaita tsarin haraji da kuma kawo sauki ga tafiyar da harakokin haraji a kasar.
A farkon watan Oktoba ne shugaban Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar tarayyar ƙudurin harajin domin domin neman amincewa. Kuma ɓangaren da ya fi jan hankalin al'ummar ƙasar, musamman daga ɓangaren arewacin ƙasar shi ne batun rabon harajin cinikayya na VAT.
Kuma gwamnonin yankin ne suka fara fitowa fili suna adawa da kudurin sabuwar dokar, suna masu cewa ana neman azurta wasu jihohi ne musamman na kudanci musamman jihar Legas da shugaban kasar ya fito.
Matsayar ƴan majalisar na arewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da alama ƴan majalisar daga shiyyar arewa sun amsa kiraye-kirayen da gwamnoninsu da sauran sarakuna da malaman addini daga yankin suka yi musu.
Kuma batun haraji ne ya haɗa kan ƴan majalisar yankin na arewa, duk da ana ganin matsin lamba ce daga shugabannin yankin na neman su yi watsi da ƙudirin sabuwar dokar harajin.
Kuma ƴan majalisar sun ƙunshi na jam'iyyar APC mai mulki da kuma sauran jam'iyyun adawa, duk da cewa akwai ƴan majalisar daga jam'iyya mai mulki da ke goyon bayan ƙudirin.
Ƴan majalisar dattawan na arewa sun ce suna iya ƙoƙarinsu ne domin kare muradun mutanen da suke wakilta, kamar yadda Sanata Buba Umaru Shehu daga jihar Bauchi ya shaida wa BBC.
"Ba mu muka fara cewa ba mu yarda ba ƙudirin harajin ba, gwamnoni da sarakuna ne suka tattauna suka ga zai cutar da mu."
"Wannan kuɗirin fahimtarsa yana da wahala, akwai buƙatar masana masu zurfin tunani da masaniya kan ilimin haraji su yi nazari,"
"Ba mu yarda da wannan kuɗirin ba, domin akwai wasu irinsa da aka daɗe ana muhawara a kan sa, amma cikin kwana biyu, uku aka kawo wannan kuma ana son mu amince," in ji Sanata Buba Umaru Shehu.
Yan majalisar na arewa sun ce dole a cire ɓangaren da ya shafi kason ƙudirin harajin da ya shafi jihohi wanda suke ganin zai yi wa jihohin arewa illa.
Sun kuma ce dole a ba al'ummar ƙasar damar fahimtar abin da kuɗirin dokar harajin ya ƙunsa kafin a zo ana neman gaggawar amincewa da shi.
"Idan har ba mu ɗauki wannan matakin ba muka bari aka amince da ƙudirin, nan gaba da mu za a yi kuka," a cewar Sanata Shehu Buba Umar.
A ɓangaren majalisar wakilan Najeriya da aka ɗauki matakin dakatar da muhawara game da ƙudirin dokar harajin, Hon Muhammad Bello Sehu Fagge ya ce matsin lamba ce ta sa aka dakatar.
"Mun lura da yadda al'umma suna nuna fushin su da wannan ƙuduri da kuma yadda limamanmu suka ɗauki al'amarin ana ta maganganu shi ya sa muka dakatar," in ji Hon Muhammad Bello Sehu Fagge.
Ya kuma ce ba da yawun bakinsu aka amince da ƙudurin ba har ya tsallake karatu na biyu.
Yanzu dai za a zura ido a ga ko matakin da ƴan majalisar na arewa suka ɗauka zai yi tasiri ga aniyar gwamnati Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da amincewa da ƙudirin harajin bayan ta yi watsi da shawarar majalisar kula da tattalin arzikin ƙasar da ta nemi a jingine kuɗirin










