A daina saka wayar da ta faɗa ruwa cikin shinkafa - Apple

Asalin hoton, getty images
Kamfanin Apple, wanda ke ƙera wayoyin hannu na iPhone ya bayar da shawarar a guji busar da wayar iPhone a cikin buhun shinkafa idan ta faɗa ruwa, duk da shaharar da wannan ɗabi'ar ta yi.
Masana dai sun dade suna gargadi kan amfani da wannan dabarar ta busar da waya cikin buhun shikafa domin gwaje-gwaje sun nuna rashin amfanin hakan.
Amma kuma yanzu, Apple da kansa ya fitar da bayanai da gargadi ga masu amfani da wayoyin kamfanin ƙirar iPhone cewa amfani da shinkafa wajen busar da waya na iya sanya ƙananan ƙwayoyin hatsin su lalata wayar.
A madadin haka, kamfanin ya bayar da shawarar cewa mutane su rika fitar da duk wani ruwa a hankali ta hanyar buga wayar a hankali a tafin hannu yayin da wurin saka caji ke fuskantar ƙasa, daga nan sai a bar wayar ta bushe.
Duk da cigaban da aka samu wajen ƙera wayoyi na zamani amma har yanzu ana amfani da tsofaffin dabaru wajen gyara su idan suka lalace.
Bugu da ƙari, Apple ya yi gargaɗi game da yin amfani da abu mai zafi wajen busar da wayar, kamar amfani na'urar busar da gashi da dai makamantan su.
Kamfanin ya kuma yi gargaɗi kan cusa abubuwa kamar su auduga ko tawul ɗin takarda a cikin wayar da sunan busar da ita.
Maimakon haka, ana ƙarfafa gwiwar masu amfani da wayoyin Iphone da su bar wayar a wuri maras danshi inda iska ke kaɗawa kafin su mayar da ita caji.
Shafin intanet na MacWorld, wanda shi ne ya gano sabon shafin da aka wallafa sabbin shawarwarin, ya nuna cewa ba za a buƙaci irin waɗannan shawarwari ba a anan gaba saboda sabbin fasahohin ci gaba da za a ɓullo da su a harkar ƙera waya.
Hakan zai faru ne kasancewar sabbin wayoyi hannu na yanzu na iya jure danshin ruwa.
Duk ƙirar wayar iPhone daga iPhone 12 na iya jure nutsewa a ruwa na mita shida har zuwa mintuna 30.
Amma da wannan yanayi na hauhawar farashin kayyayaki a kasuwannin duniya da kuma tsadar rayuwa, mutane da dama na buƙatar irin waɗannan shawarwari kan abin da za su yi idan wayarsu ta faɗa cikin ruwa ko wani abu na ruwa haka—da abubuwan da ba za su yi ba










