Tsadar rayuwa: 'Ba mu san inda za mu saka kanmu ba'

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ....
    • Marubuci, Isidore Kouwonou avec Simon Gongo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar et Ouagadougou
  • Lokacin karatu: Minti 3

A cikin makonnin da suka gabata Burkina Faso ta shiga wani yanayi na tashin farashin kayan masarufi a kasuwanni.

Farashin wasu kayan sun nunka ko ma fiye da haka, lamarin da ya bar al’ummar ƙasar cikin ruɗani.

A kasuwar Paglayiri da ke kudancin Ouagadougou, babban birnin ƙasar, mutane da dama sun ƙaurace wa kasuwa, abin da ke nuna cewa akwai ƙarancin masu saye da sayarwa waɗanda yanzu ba su iya zuwa yin cinikayya.

Lucie Yerbanga, wadda ta mallaki shago a kasuwar ta ce lamarin ya fara ƙamari ne tun a watan Oktoban da ya gabata. “Abin ya fi ƙarfinmu. Shinkafa da man girki da komai ma ya yi tsada. Ba mu san ina za mu saka kanmu ba,” kamar yadda ta shaida wa wakilin BBC.

Ta ce yanzu kayan masarufi sun fi ƙarfin talakan ƙasar.

A bayanin da ta yi wa BBC, ta ce litar man girki wadda a baya ake saya kan kuɗi CFA 1,000 yanzu ta yi tashin gwauron zabi zuwa CFA 1,400.

Ta ce “Mukan sayi buhun shinkafa mai nauyin 50kg kan CFA 22,000 a baya, amma a yanzu ya kai CFA 25,000 ko ma 26,000.”

Lamarin ya jefa hatta ƴan kasuwa cikin ƙaƙa-ni-ka-yi kasancewar ba su samun ciniki yadda ya kamata.

“Ka gan mu zaune a nan, babu abin da muke yi, babu abin da muke sayarwa. Abin ya tsananta,” in ji Yerbanga.

‘Mun kasa gano abin da ya haifar da hakan’

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ..

A wani shagon sayar da kayan abinci da ke cikin kasuwar ta Paglayiri, Marturin Zida ya fito ransa a ɓace saboda irin abin da ya gani.

Yana ganin cewa babu wata hujja da za a riƙa samun tashin farashi haka babu gaira babu dalili.

“Babu wani tsayayyen farashi, kullum abubuwa na sauyawa,” in ji shi.

Yana ganin cewa duk wani ɗan Burkina Faso wanda wanda kudin shigarsa bai kai CFA 100,000 ba, ba zai iya rayuwa yadda ta dace ba.

Hatsi da shinkafa da man girki duk sun tashi a kasuwa.

“Rayuwa ta yi tsada a nan. Yanzu za ka sayi abu amma idan ka dawo washegari sai ka ji farashin ya canza,” in ji Mista Zida.

Hujjojin da gwamnati ta bayar

...

Asalin hoton, Ministère de l'Industrie, du Commerce et de l'Artisanat

Bayanan hoto, ...
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumomi ba su kawar da kai daga halin da mutanen ƙasar ke ciki ba, wanda ke ƙara tsananta a kullum.

Olivier Kiema, daraktan sanya ido kan tattalin arziki a ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ya ce tashin farashin kayan masarufin ba laifin ƴan kasuwa ba ne kadai.

“A lokacin da muka yi bincike, mun gano cewa, misali a ɓangaren tsadar man girki, kashi 20 cikin ɗari na man girki ne kawai ake samarwa a cikin gida, inda ya bayyana cewa kashi 70 cikin ɗari na man girki da al’ummar ƙasar ke amfani da shi ana shiga da shi ne daga Indonesia da Togo da kuma Ivory Coast.

“Saboda haka nan tashin farashin man girki da aka samu a ƙasar ya samo asali ne daga ƙasashen ƙetare,” in ji shi.

Bayanin ya ƙara da cewa akwai abubuwa uku da suka haddasa tashin farashin a cikin gida:

“Na farko akwai tashin farashin dala. A watan Oktoba ana canjin dala ɗaya ne kan CFA 597 yayin da yanzu kuma ake canjin dala ɗaya kan CFA 637.”

Ya ƙara da cewa akwai kuma ƙarin tsadar man girkin shi kansa, sai kuma farashin sufuri.