Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban kwallon Faransa ya nemi afuwar Zidane
Shugaban hukumar kwallon kafar Faransa Noel le Great ya nemi afuwar kan ‘’ kalaman da ba su dace ba’’ da ya yi a kan ko Zinedine Zidan na sha’awar horar da tawagar ‘yan wasan kasar.
A hirar da ya yi da wani gidan rediyon Faransa, Le Graet mai shekara 81 ya ce “ko da Zidan ya kirashi ba zai dauki wayarsa ba”.
Le Graet a ranar Litinin ya ce maganar da ya yi “ba ra’ayinsa bane”
Kocin Faransa Didier Deschamps ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi har zuwa 2026 a ranar Asabar.
"Ina son ayi man afuwa saboda wadannan kalamai, wadanda kwata-kwata ba su yi dai-dai da ra’ayi na ba ko ra’ayina a kan dan wasan da ya kasance a baya da kuma kocin da ya zama ba ," in ji Le Graet.
"Na yi hira da wani gidan rediyon na Faransa RMC wanda bai kamata na yi ba saboda suna neman su janyo ce-ce ku-ce ta hanyar adawa da Didier da kuma Zinedine Zidane, shahararun ‘yan wasan kwallon kafa na Faransa.
" Na yarda cewa na yi wasu kalamai marasa dadi wadanda suka haifar da rashin fahimta."
Zidane ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 a matsayin dan wasa tare da Deschamps da kofunan gasar La Loga biyu da kofin zakarun Turai guda uku a matsayin kocin Real Madrid kafin ya bar kungiyar a bara.
Dan wasan gaban Faransa da Paris St Germain Kylian Mbappe ya bayyana kalaman Le Graet's a matsayin " rashin mutumci ".
Ministar wasanni ta Faransa. Amelie Oudea-Castera ta bukaci Le Graet da ya nemi gafara " saboda tamkar rashin girmamawa ne".
Real Madrid ta fitar da sanarwa da ta nemi a "ayi gyra cikin gaggawa" bayan kalaman Le Graet's .
Deschamps shi ne ya jagoranci Faransa zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya karo na biyu a watan Disemba lokacin da ta sha kaye a hannun Argentina a bugun Fenariti